Connect with us

Labaran Najeriya

Boko Haram: Shugaba Buhari Ya Roki ‘Yan Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Ranar Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari

An yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yarda ‘yan ta’adda su raba kasar biyu ta hanyar addini.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya sanya wa hannu da kuma aka bayar ga manema labarai a yau.

Buhari ya bayyana hakan ne bayan kisan da ‘yan ta’addan Islamic State West Africa (ISWAP) suka wa wasu kiristoci da musulmaia cikin makon nan.

Bayanin Shugaba Buhari na kamar haka a ƙasa:

“Na yi matukar bakin ciki da kisan wadanda aka yi garkuwa da su a hannun mutane marasa tausayi, marasa tsoron Allah, gungun masu kisan da suka yiwa Musulunci mummunan suna ta hanyar kisa.”

“A kowace yanayi, bai kamata mu bar ‘yan ta’adda su raba mu ta hanyar karkatar da kirista a kan musulmai saboda wadannan masu kisan gilla ba, saboda wadannan masu kisa a kowace hanya basu wakilcin Musulunci da miliyoyin sauran musulmai masu bin doka da oda a fadin duniya.”

“A matsayina na Shugaban kasa, tsaron gamaiyar dukkan ‘yan Najeriya shine babban damuwata kuma mutuwar wani kirista ko musulmin abun bakin ciki ne a gareni sosai.”

Shugaban ya ce ‘yan ta’addar ba su da wata manufa ta a bayyane, iya kawai mugunta ta hanyar kisan da ba ta dace ba ga mutane, sabanin koyarwar addinin Islama, wanda ya haramta kisan kiyashi.

“Babu wani musulmin kwarai da zaiyi ihun ‘Allahu Akbar’ yayin kashe mutane marasa laifi, sharrin da Alkur’ani mai girma yake yin Allah wadai da shi.”

“Wadannan wakilai na duhu makiya ne da ci gaban kasarmu a baki daya kuma ba su bar kowa ba, ko da musulmi ko kirista, a saboda haka, bai kamata mu bari su rarrabe mu da juya hankalinmu ga juna ba.

“Manufar wadannan mutanen kawai itace haifar da rudani da yada rashin yarda tsakanin musulmai da kirista, duk da cewa basa wakiltar maslahar musulmai ko musulinci.

“Yayin da na la’anci wannan sharri, ina mai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa wannan gwamnatin ba za ta rage masu tsaronta ba a yakin da ake yin ta’addanci, kuma za mu ci gaba da kara himma wajen karfafa hadin gwiwa kasa da kasa domin karya lagon wadannan masu aikata mugunta.” inji Shugaba Buhari.