#EidAlFitr2019: ‘Yan Sanda sun kame mutane 55 da suka tada fada a Jihar Bauchi

Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Bauchi a yau Alhamis, 6 ga watan Yuni 2019 sun kame mutane 55 da ake zargi da kasancewa a fadar da aka yi a ranar Laraba da ta wuce, wajen hidimar sallar Hawan Daushe.

Bisa bayanin kakakin yada yawun Jami’an tsaron Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar, ya bayyana da cewa hukumar su ta kame mutanen ne da kuma ribato makamai da ke a hannun su. Ya fada cewa fadar ya tashi ne a lokacin da ake hidimar Dubar, dadai lokacin da wakilan sauratar yankin Bauchi ke ziyarar Gwamnan Jihar, Bala Mohammed, a nan gidan gwamnatin Jihar da ke a Bauchi.

“Fadar ya tashi ne tsakanin wata kungiyar ‘yan farauta da ke biye da wakilin Darazo da kuma wata kungiya ta shiyar Duguri, a yayin da ake cikin hidimar Durbar.”

“A garin hakan ne aka kashe wani daga karamar hukumar Darazo mai suna Auwalu Sadau ‘M’, aka kuma yiwa Usama Musa daga shiyar Duguri a karamar hukumar Alkaleri da kuma Zakari Suleiman daga karamar hukumar Darazo, hade da wasu mutane 12 suka yi mugun raunuka sakamakon harin” inji DSP Kamal.

Ya kara da cewa hukumar Jami’an tsaron Bauchi sun riga sun lafar da fadar a jagorancin Operation Puff Adder.\

“Hukumar ta amshe makamai daga hannun mutane 55 da aka kame, an kuma haura da wadanda suka yi rauni a Asibitin ATBUTH don basu kulawa da musanman.”

Rahoto ta bayar da cewa Gwamnan Jihar, Bala Abdulkadir Mohammed ya riga ya ziyarci mutanen a asibiti, ya kuma gargadi al’ummar shiyar da kasance da zaman lafiya.

Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa cewa Yan Hari da Bindiga sun kashe akalla mutane 16 a Ranar Sallar Eid-Al-Fitr a Zamfara

#EdiAlFitr2019: An Kashe Mutum Daya da yiwa wasu rauni a hidimar Durbar da aka yi a Jihar Kano

Hidimar Durbar ta Hawan Daushe da aka yi a Jihar Kano ya karshe da Farmaki a yayin da aka kashe mutum guda
a ranar Sallar Eid-El Fitr da Eid-El- Kabir, Laraba da ta gabata.

Haka kazalika aka bayyana da cewa mutane biyu kuma sun yi muguwar rauni a fadar, jami’an tsaro kuma suka samu kame mutane shidda.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa hakan ya faru ne a wakilcin Sarkin Kano, Malam Muhammad Sanusi II, a hidimar duk da rashin bayyanar Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Ko da shike an bayyana cewa Ganduje ya tafi wata hidima ne.

KARANTA WANNAN KUMA; Babbar Motar Tirela ta hau kan wani Mutumi mai sayar da kaya a kan hanya a Kaduna

Abin Al’ajabi! Kalli yada aka gano da Bu’tocin Alwalla a tsakar wata Icce

Wani sananne da Shahararran dan hadin fim a Najeriya mai suna Ernest Obi ya rabar da wata bidiyo a layin yanar
gizon nishadi da barin kowa da baki bude.

Naija News ta gane da cewa bidiyon na dauke ne da wata abin mamaki, a cikin bidiyon, a nino yadda butocin
Alwalla fiye da dari ke fadowa a yayin da ake sarar wata Icce.

A bayanin Mista Obi, ya ce; “Da ace wannan ya faru ne a cikin shirin fim ta Nollywood ko kuma wata fagen hadin
wasan kwaikwayo, da sai ace ai baiyiwuwa hakan ya tabbata.

Ya bayyana da cewa Iccen ne ke da sanadiyar butoci da yawa da suka bata a baya a Masalacin da ke a wajen.

Ko da shike wasu na zargin cewa watakila wasu ne ke ta jefa butocin a tsakar iccen tun da dadewa.

A cikin bidiyon, an nuno yadda wani mutumi ke fitar da butoci daga tsakar iccen a yayin da ake yankar iccen da
injimin yankar itace.

Haka kazalika aka nino yadda mutane ke labe a gefe da leken yadda ake fitar da butocin da kuma yankar iccen.

Kalli Bidiyon a kasa kamar yadda aka rabar a layin Twitter;

Hukumar Tsaro sun kame wani mutum mai taimakawa Boko Haram a Maiduguri

Hukumar Tsaro Civil Defence Corps (NSCDC) da ke a Jihar Borno, a ranar Laraba 5 ga watan Yuni ta sanar da kame wani mutumi mai suna Aliyu Muhammed, mai shekaru 24 ga haifuwa da zargin samar da miyagun makamai da kayan hadin Bama-Bamai ga ‘yan ta’addan Boko Haram da ke a Maiduguri.

Naija News Hausa ta gane da rahoton ne bisa bayanin Mista Ibrahim Abdullahi, Kwamandan Hukumar Tsaro ta Civil Defence ga manema labaran NAN, a Maiduguri, babban birnin Tarayyar Jihar Borno.

Mista Abdullahi ya bayyana da cewa rukunin tsaron su ta gane da Aliyu ne tun ranar 25 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata, aka kuma kame shi a yayin da yake batun kai kayan hadin miyagun makamai ga ‘yan Boko Haram, kamar yadda ya saba yi.

Ka tuna cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sun ribato Mata 29 da Yara 25 daga rukunin Boko Haram.

Bisa binciken hukumar NSCDC, sun gane da cewa Aliyu kan nemo wa ‘yan ta’addan Baturorin waya, Agogon hannu da kuma Kwamfuta (Laptop), wanda suke amfani da su wajen hadin bama-baman IEDs.

An kara da cewa lallai Aliyu ya dade da yin aikin, mutane sun sanshi ne da aikin tukin motar KEKE-NAPEP a cikin gari, amma yana da liki da ‘yan Boko Haram ba tare da sanin su ba.

Ha kazalika aka gane cewa yana da asusun ajiyar kudi da dama inda Boko Haram ke aika masa kudade don biyan sa ga aikin da yake masu.

Shugaban hukumar tsaron Civil Defence, Mista Mohammed ya bayyana cewa zasu bayar da Aliyu ga Rundunar Sojoi ta 7 Division Garison, don ci gaba da bincike akan dan ta’addan.

Babbar Motar Tirela ta hau kan wani Mutumi mai sayar da kaya a kan hanya a Kaduna

Wata mumunar hadari ta dauke rayuwar wani mutumi a ranar Talata, 4 ga watan Yuni a Jihar Kaduna

Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda mota ya take wani mutumi wanda ba a samu gane da sunansa ba kan babban hanya a tsakar Kaduna.

An bayyana a labarai da cewa motar ta hau mutumin ne a yayin da yake sayar da kayan sawa a tsakar motoci masu yawa a babban hanya.

Bisa bayanin wani da ya samu ganawa da hadarin, ya fada da cewa Babbar Motar Tirelar da ta hau mutumin  ta tsaya ne tare da wasu motoci da ke a kan hanyar, a yayin da dukan su ke jirar wutar kan hanya ta yada kalan ruwan ganye, watau alamar daman tafiya.

“Bayan da wutar dokar hanya ta haska da kalan ruwan ganye sai direbar babban motar ya kafa kai ga tuki, kwaram sai ya hau mutumin ba tare da sanin cewa yana gaban motar ba da kokarin sayar wa wani kaya” inji shi.

“Motar ta take mutumin ne har da watsar da kwakwalwansa da hanji duka”

Ya bayyana da cewa an riga an kwase gangar jikin mutumin an kuma kai a gidan ajiyar gawa”

Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa Kimanin mutane Goma-Shatara suka rasa rayukan su a wata hadarin Motar Bus da ya faru a wata shiya ta karamar hukumar Gwaram, a Jihar Jigawa.

Wani ya Kashe Makwabcin sa a Jihar Neja da laifin Lalata da Matarsa

Wani mutumi mai shekaru 30 da haifuwa a Jihar Neja ya kashe Makwabcin sa

Audu Umar, wani mazaunin kauyan Wawa daga karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja, ya kashe makwabcin sa Abubakar Muhammadu, mai shekaru 21 ga haifuwa da zargin cewa yana kwanci da matarsa.

Bisa rahotannai da aka bayar ga Naija News Hausa, duk da cewa Audu na a kulle a Ofishin Jami’an tsaro, bai nuna alamar danasani ba.

“Banyi danasani ba da kashe Muhammadu saboda ya saba da neman kwanciya da matan aure a shiyarmu” inji Audu.

Mutumin da ya Kashe Makwabcin Sa a Jihar Neja

“Ina da cikakken murna da dauke rayuwan Muhammadu, ina kuma a shirye don fuskantar shari’a akan yin hakan” inji shi.

Ya kara da cewa yana da murnan ganin Muhammadu ya mutu kamar ‘yar chako. “Ba zai sake kwanci da matana ba, Idan duniya ta sake juyowa ba zai kara yin hakan ba” inji shi.

Bisa bayanin da aka bayar, matar Audu, Malama Hassana tayi karar marigayi Muhammadu ga maigidanta a lokatai da yake bukatar kwanci da ita, duk da cewa ta hana shi da hakan.

“Sau da dama ya gargadi Muhammadu da janyewa daga wannan mumunar halin na bukatar kwanciya da mata na ko kuma matar aure da ke a kauyan, da kuma na gane da cewa yaki amince da hakan, da na fusata sai na bi shi da sarar adda har ga kashe shi” inji Audu.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron yankin, Mohammad Abubakar, ya bayyana da cewa hukumar su na kan bincike ga lamarin, idan kuma sun kamala bincike sai a mikar da Audu ga Kotun Shari’a.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Wani mutum a Jihar Neja, ya kashe Makwabcin sa don yana masa ba’a da zage zage.

#EidAlFitr2019: Barka da Sallah daga Naija News Hausa

Naija News Hausa na Maku Barka da Sallah!

Gaisuwa ta musanman ga masoya da masu lasar labarai a shafin Naija News Hausa, muna mai taya ‘yan uwa Musulumai duka murna da kai ga karshen hidimar Azumin watan Ramadani da aka kamala a ranar jiya Litini, 3 ga watan Yuni 2019, a cikar rana 29 ga Ramadan.

Kamar yadda muka sanar a baya a Naija News Hausa cewa Sarkin Musulumai, Mai Martaba Sultan na Sokoto, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bada wasu lambobi da sunaye da za a Kira idan an gana da Fitar Watan Shawwal.

A tabbacin ganawa da watan ne aka sanar a daren jiya Litini da cewa yau ya kama 1 ga Watan Shawwal 1440 AH, wanda ya bayyana cikar rana 29 ga Ramadani, 1440 AH.

A hakan ne muke nuna murna da cikar Azumin Ramadani da kuma kai ga ganin Sallar Eid Al-Fitr ta shekarar 2019.

Babban Addu’ar mu itace, Allah da yasa aka fara azumin da kuma kare ta lafiya ya bamu kwanciyar hankali, zaman lafiya, ci gaban shugabanci da kuma abin biyan bukata dan Adam a kasar Najeriya da duniya gaba daya.

Allah ya sa kuma mu ga badi cikin koshin lafiya, duk abinda kowa ya roka kuma a hidimar Ramadani, Allah ya biya masa bukatun sa.

BARKA DA SALLAH!  BARKA DA SALLAH!!  BARKA DA SALLAH!!!

APC ta Jihar Zamfara sun kori Marafa da wasu mutane biyu kuma

Jam’iyyar shugabancin kasar Najeriya, APC ta Jihar Zamfara sun kori Sanata Kabiru Garba Marafa da wasu mutane biyu daga Jam’iyyar, akan laifin makirci ga Jam’iyyar.

Naija News Hausa ta gane da cewa Jam’iyyar sun kori sanatan ne da ke wakilci a Zamfara Central a gidan Majalisa ta Takwas, hade da Hon Aminu Sani Jaji da kuma Mal Ibrahim Wakkala Liman.

An sanar da korar sanatan ne a wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai a birnin Abuja, ranar Litini da ta wuce, daga bakin Sakataren Sadarwa na yankin, Shehu Isah.

Matakin Jam’iyyar ga dakatar da Marafa ya kasance ne bisa ga zargin cewa ‘yan siyasan sun karya dokar Jam’iyyar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawallen-Maradun ya bada Naira Miliyan N83m don sayan Shanayan Sallar Eid El-Fitr.

Bisa bayanin Mista Idris Yusuf Gusau, Daraktan Sadarwa ga Jihar ya bayyana cewa shanaye 750 da za a saya din za a rabar da su ne ga ragaggagu, gwamraye, yara marasa iyaye da ke a Jihar, don taimaka masu a wannan lokacin lokacin hidimar Sallah.