Connect with us

Uncategorized

Wani ya Kashe Makwabcin sa a Jihar Neja da laifin Lalata da Matarsa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani mutumi mai shekaru 30 da haifuwa a Jihar Neja ya kashe Makwabcin sa

Audu Umar, wani mazaunin kauyan Wawa daga karamar hukumar Borgu ta Jihar Neja, ya kashe makwabcin sa Abubakar Muhammadu, mai shekaru 21 ga haifuwa da zargin cewa yana kwanci da matarsa.

Bisa rahotannai da aka bayar ga Naija News Hausa, duk da cewa Audu na a kulle a Ofishin Jami’an tsaro, bai nuna alamar danasani ba.

“Banyi danasani ba da kashe Muhammadu saboda ya saba da neman kwanciya da matan aure a shiyarmu” inji Audu.

Mutumin da ya Kashe Makwabcin Sa a Jihar Neja

“Ina da cikakken murna da dauke rayuwan Muhammadu, ina kuma a shirye don fuskantar shari’a akan yin hakan” inji shi.

Ya kara da cewa yana da murnan ganin Muhammadu ya mutu kamar ‘yar chako. “Ba zai sake kwanci da matana ba, Idan duniya ta sake juyowa ba zai kara yin hakan ba” inji shi.

Bisa bayanin da aka bayar, matar Audu, Malama Hassana tayi karar marigayi Muhammadu ga maigidanta a lokatai da yake bukatar kwanci da ita, duk da cewa ta hana shi da hakan.

“Sau da dama ya gargadi Muhammadu da janyewa daga wannan mumunar halin na bukatar kwanciya da mata na ko kuma matar aure da ke a kauyan, da kuma na gane da cewa yaki amince da hakan, da na fusata sai na bi shi da sarar adda har ga kashe shi” inji Audu.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron yankin, Mohammad Abubakar, ya bayyana da cewa hukumar su na kan bincike ga lamarin, idan kuma sun kamala bincike sai a mikar da Audu ga Kotun Shari’a.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Wani mutum a Jihar Neja, ya kashe Makwabcin sa don yana masa ba’a da zage zage.