Uncategorized
Babbar Motar Tirela ta hau kan wani Mutumi mai sayar da kaya a kan hanya a Kaduna
Wata mumunar hadari ta dauke rayuwar wani mutumi a ranar Talata, 4 ga watan Yuni a Jihar Kaduna
Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda mota ya take wani mutumi wanda ba a samu gane da sunansa ba kan babban hanya a tsakar Kaduna.
An bayyana a labarai da cewa motar ta hau mutumin ne a yayin da yake sayar da kayan sawa a tsakar motoci masu yawa a babban hanya.
Bisa bayanin wani da ya samu ganawa da hadarin, ya fada da cewa Babbar Motar Tirelar da ta hau mutumin ta tsaya ne tare da wasu motoci da ke a kan hanyar, a yayin da dukan su ke jirar wutar kan hanya ta yada kalan ruwan ganye, watau alamar daman tafiya.
“Bayan da wutar dokar hanya ta haska da kalan ruwan ganye sai direbar babban motar ya kafa kai ga tuki, kwaram sai ya hau mutumin ba tare da sanin cewa yana gaban motar ba da kokarin sayar wa wani kaya” inji shi.
“Motar ta take mutumin ne har da watsar da kwakwalwansa da hanji duka”
Ya bayyana da cewa an riga an kwase gangar jikin mutumin an kuma kai a gidan ajiyar gawa”
Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa Kimanin mutane Goma-Shatara suka rasa rayukan su a wata hadarin Motar Bus da ya faru a wata shiya ta karamar hukumar Gwaram, a Jihar Jigawa.