Kalli Jerin Kwararrun ‘Yan Fim Na Hausa Da Muke Da Tarihin Rayuwarsu A Rubuce

Naija News Hausa a sashen mu ta Nishadi mun ruwaito da Tarihi da Takaitaccen Labarin ‘yan shirin fim a Kannywood da dama cikin ‘yan watanni da suke shige.

Na farko a jerin tarihin ‘yan kannywood da Naija News Hausa ke dauke da shi itace Fati Washa, ba son kai ko wata ban girma ba amma itace na farko da kuma wacce aka fi neman karanta tarihinta a shafin mu.

Karanta Jerin suna da Adadin labaran rayuwarsu a kasa;

1. Fati Washa

Fatima Abdullahi Washa sananiyar akta ce a Kannywood. Sunar ta a filin wasa itace Fati Washa.  an haife ta ne a Watan Biyu 21, 1993, a Jihar Bauchi. a santa da sunaye kuma kamar haka; Tara Washa ko kuma Washa. A shekara ta 2018, Fati Washa na da shekaru 25. Kuma bata da Aure. Kyakyawa ce kuma da hasken jiki, Fati Washa tana daya cikin masu tsarin fim wanda ake fahariyya da su a Kannywood.

Akwai sani da cewa ita Kyakyawar yarinya ce kuma daya daga cikin yan wasan fim dake da tsadar kamu a Kannywood. Da yawa a cikin masoyan ta kan so ta a nishadi da kuma neman ta a facebook da sauran fillin nishadi don darajata ta ga aikin ta. Ci gaba da karanta labarin Fati Washa.

2. Ali Muhammad Idris (Ali Art Work)

Dan matashin mai suna Ali Muhammad Idris da aka fi sani da Ali Artwork, an haife shi ne kuma ya girma ne Jihar Kano, a Yankin Tarauni ta Jihar Kano.

Kamar yadda na san kuna muradi na so gane ko shi dan shekara nawa ne

An haife Ali Muhammad Idris ne a ranar 1 ga Watan Janairu, a shekara ta 1992.
Ya fara makarantar firamare ne a wata Makaranta mai Suna Unguwan Uku Firamare Sukul a shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2005. ya karasa da karatun sa a Makarantar sakandare farko watau (JSS 1) a Wata Makarantar sakandare ta gwamnati daga shekara ta 2005 zuwa 2008,  bayan kammala wannan ya samu dace da ci gaba da karatun sakandaren a wata sakandare na Kundila, watau GSS Kundila daga Shekara ta 2008 zuwa 2011. Ci gaba da karanta labarin Ali Art Work.

3. Ummi Ibrahim – Zee Zee

An haifi Ummi ne a Jihar Borno a shekara ta 1989. Tsohon ta Ba’Fullace ne, uwar kuwa ‘yar Arab ce.

Ummi ta bayyana shahararun ‘yan wasa da ta ke ji d su da kuma take koyi da su sosai wajen shiri.

“Wadanda na ke ji da su kuma na ke koyi da su a filin wasan Kannywood sune kamar haka; Marigayi’a Aisha Dan-Kano da Marigayi Rabilu Musa Dan-Ibro. muna ba wa juna girma sosai da gaske, Allah ya gafarta masu” in ji ta a wata ganawa da ta yi da manema labaran (Information Nigeria) shekara da ta gabata. Ci gaba da karanta labarin Zee Zee.

4. Sani Danja

Sani Danja, kamar yadda aka fi sanin sa da suna, daya ne daga cikin shaharrarun ‘yan shirin fim ba Kannywood da ake ji da su.

Ainihin sunansa Danja ita ce; Sani Musa Abdullahi, ko kuma Sani Musa Danja.

An haifi Sani Danja ne a ranar 20 ga watan Afrilu ta shekarar 1973 a nan garin Fagge, ta Jihar Kano, a kasar Najeriya. Bincike ya bayyana da cewa Sani Musa Abdullahi ya samu likin Danja ne a lokacin da yake karami, dalilin suna kuwa itace irin halin da Sani ke da shi na rashin ji a lokacin. Kawai abokanan wasa suka laka masa sunan ‘Danja’ wanda a yau ko ina ka kira Sani Danja an riga an gane ko da wa kake. Ci gaba da karanta labarin Sani Danja

5. Rahama Sadau

An haifi Rahama Ibrahim Sadau ne a ranar 7 ga watan Disamba, a shekarar 1993 kamar yadda ‘Wikipedia’ ta bayar. Ta kuma yi zaman rayuwarta ne da iyayen a Jihar Kaduna tun daga haifuwa.

Rahama Sadau tayi karatun jami’a na farko ne a Makarantan Fasaha ta Jihar Kaduna da aka fi sani da (Kaduna Polytechnic), inda ta karanta ‘Business Administration’ a matsayin kwas na ta.

Sadau, ta kara da karatun ta na karanta kwas din ‘Human Resource Management‘ a wata babban Makarantar Jami’ar Eastern Mediterranean University in Northern Cyprus a shashin bincike akan sana’a da tattalin arziki. Ci gaba da karanta labarin Rahama Sadau.

6. Maryam Booth

Maryam Ado Muhammed, wata Kyakyawa da aka fi sani da Maryam Booth, Shahararra ce a fagen wasan kwaikwayo na Kannywood, Tana kuma da Fasaha wajen aikin Dinke-dinke.

Maryam Ado Muhammed ‘yar haifuwar Jihar Kano ce a arewacin Najeriya, an kuma haife ta ne a ranar 28 ga Watan Oktoba, a shekaran 1993.

Mahaifiyarta Maryam kuwa Ita ce, Zainab Booth, Ita ma kwararra ce kuma daya daga cikin wadanda suka dade a shirin wasan kwaikwayo na Kannywood. Haka Kazalika dan uwan Maryam, watau Ahmed Booth, shi ma Gwarzo ne a filin hadin Fim na Kannywood.

Ko da shike Kaka ta Mace ga Maryam Fulani ce, amma Kakanta namiji dan Turai ne, daga Scotland. Ci gaba da karatun labarin Maryam Booth.

7. Umar M. Sharif

Umar Muhammadu Sharif yana daya daga cikin Shahararrun mawaƙan hausa masu mahimmancin kwarari da gaske.

Sharif ba Mawaki ne kawai ba, Dan kasuwanci a fagen wasa, yana kuma da kyautannai lambar yabo mai yawa da ya karba a fagen shiri.

An haifi Sharif ne a shekarar 1987, ya kuma yi karatun Makarantar Firamare da Sakandiri ne a garin su, Rigasa ta Jihar Kaduna.

Umar ya bayyana da cewa shi ya kasance ne dalibi mai mahimmanci kuma tun lokacin yarantakarsa, abin da ya sa shi cikin raira waƙa shi ne wani abin da ya faru tsakanin shi da ƙaunarsa na farko, kamar yadda ya fada wa BBCHausa. Ci gaba da karatun labarin Umar M. Sharif.

8. Ali Jita

Ali Jita shahararran mawaki ne mai zamaninsa a Kano, sananne ne kuwa a wake-wake a fagen shirin finafinan Hausa, kuma ya shahara kwarai da gaske a yawancin finafinan hausa.

Ainihin sunan sa itace Ali Isa Jibril, kuma an haife shi ne a unguwar gyadi-gyadi a cikin badalar Kano dake a Arewacin Najeriya.

Ali yayi karatun farkon sa na Firamare ne a wata makarantar da Sakandare duk a birnin Legas, a wata makarantar sojojia, kamin dada ya bar Legas zuwa brinin Tarayyar kasa, Abuja. Ci gaba da karanta labarin Ali Jita.

9. Bilikisu Shema

Kyakkyawa da kuma shahararriyar, Bilkisu asalinta ‘yar Jihar Katsina ce. An haifi Bilikisu Shema ne a ranar 28 ga Watan Yuli a shekarar 1994.

Fitacciyar, Shema ta fara karatun ta na firamari ne a makarantar Isa Kaita College of Education, bayan nan ta shiga sekandari a Government Day Secondary School Dutsin-Ma.

Naija News Hausa ta gaza da samun tabbacin karatun babban jami’ar jarumar a wannan lokaci, idan hakan ya samu, zasu sami karin bayani.

Shema dai a cikin tashe a fagen fim a wannan lokaci, ita ce matashiyar jaruma wadda tauraronta yake haskawa. Ci gaba da karanta labarin Bilikisu Shema.

10. Jamila Nagudu

A takaice dai, Jaruma Jamila Nagudu ‘yar wasan finafinan Hausa ce wacce aka Haifeta a ranar 10 ga watan Agusta.

Jamila Umar Nagudu a nata bangaren Sarauniyar Kannywood ce, ma’ana, ita babbar jaruma mace ne a fagen shirya fina-finan Hausa, watau Kannywod wacce take da hedkwatarta a Kano, arewacin Najeriya.

Jarumar ta shiga fagen masana’antar fim na Hausa ne shekaru da yawa baya, amma ‘yan shekaru da suka gabata, babban Froduza na fina-finai, Aminu Saira ya sanyata a cikin fitaccen fim din da aka yi wa take ‘Jamila da Jamilu’, watau tun a fim dinne tauraron jaruma Jamila ya haska da bayyana ta ko ta ina saboda irin kwarewa da taka rawar gani a fim din. Ci gaba da karanta labarin Jamila Nagudu.

11. Nafisat Abdullahi

Nafisat Abdulrahman Abdullahi, wadda akafi sani da Nafisat Abdullahi, kyakyawa ce da kuma shahararrar ‘yar shirin fim a Kannywood, watau kamfanin hadin fim na Hausa a Najeriya.

An haifi Nafisat ne a ranar 23 ga watan Janairu ta shekarar 1991 a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

Nafisat ita ce ‘ya ta hudu ga Mallam Abdulrahman Abdullahi, wani dillalin motoci da kuma dattijo masu ruwa da tsaki a kasar.
Naija News Hausa ta fahimci cewa kyakyawar tayi karatun ta na farko ne a Makarantar ‘Air Force Private School’ a nan Jos, bayan nan ta koma Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, inda ta shiga makarantar Sakandare ta Gwamnati, Dutse, Abuja. Ci gaba da karanta labarin Nafisat Abdullahi.

Ka lasa shafin Nishadi a Naija News Hausa a koyaushe don samun labaran ‘yan shirin fim na Hausa da kuma manyan labaran Nishadi ta kowace rana.

Kannywood: Ali Jita Ya Lashe Kyautan Mafi Kwarewar Mawaki A Shekarar 2019

Shahararran mawakin Hausa da aka fi sani da suna Ali Jita, ya lashe kyautan kwarewa da zakin murya wajen wake-wake a shekarar 2019.

Mawakin da bincike ya nuna da tsunduma a harkar wake-waken Hausa tun daga shekarar 2009 ya bayyana murnansa na lashe kyautan ne a wata sako da ya wallafa a shafin yanar gizon nishadi ta Twitter.

Sakon na kamar haka;

“A gaskiya an karrama ni, wannan shi ne babbar kyauta mafi girma da aka taba yi a Arewa, ina alfahari da kasancewa wakiltar abin da na tsayawa, kuma insha Allah Zan ci gaba da sanya ku ga alfahari, Nagode.”

Ga sakon a kasa kamar yadda Ali da kansa ya wallafa a turance;

 

KARANTA WANNAN KUMA; Takaitaccen Labari da Rayuwar Babban Mawaki Ali Jita

Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya Sun Yi Hadarin Mota A Jihar Ebonyi

‘Yan sanda sun kubuta bayan fadawa cikin wani Hatsari a Ebonyi

Wasu ‘yan sanda a jihar Ebonyi sun samu raunuka bayan da suka afka cikin wani mumunar hadari, a yadda wasu mazauna yankin da ke wucewa suka ceto su.

An kubutar da ‘yan sandan ne daga hannun wasu masu hali nagari bayan sun shiga cikin wani hadari a kan hanyar barikin soja na Nkwagu da ke jihar Ebonyi.

Kodashike, babu daya daga cikin jami’an tsaron da ya mutu a hadarin wanda ya faru a farkon safiyar Disamba 1, amma dai sun sami raunuka daban-daban.

An sanar da hakan ne da farko a kan layin yanar gizon nishadi da sadarwa ta Facebook na wani mai suna, Jaykizz Adeleke, wanda ya rabar da hotunan hatsarin motar ya ce;

“Ku dubi abin da ya afku sakamakon yawar gudu da hanzari … Hadarin ya faru ne a kan hanyar Barikin Sojoji ta Nkwagu a jihar Ebonyi… A safiyar yau da karfe 8:55 na safe

“Wadannan jami’an ‘yan sanda suna so ne su hade da Kakanninsu ko? amma Allah ya kubutar dasu daga mutuwa … a yau farkon ranar Disamba ga 2019.”

Kalli Hotuna a Kasa;

Sabuwar Waka: Sirrin Soyayya – daga bakin Ahmed Musa Oxford da Rukky Ilham

Kalla ka sha dadin nishadin sabuwar wakar hausa da Ahmad Musa Oxford hade da Rukky Ilham suka fitar ba da jimawa ba.

Naija News Hausa ta gano wannan ne a layin yanar gizon nishadarwa ta Kannywood, watau shafin nishadi ta kungiyar shahararrun masu shirin fim na hausa.

Kalli bidiyon wakar a kasa;

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 20 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 20 ga Watan Satunba, 2019

1. Majalisar Wakilai sun Umarci CBN Da dakatar da Sabon Tsarin Kudi

Majalisar wakilan Najeriya ta karo na 9 ta umarci Babban Bankin Tarayyar Najeriya da dakatar da shirinta kan sabon manufar tsarin ajiyar kudade.

Ka tuna cewa Naija News ta ba da rahoton cewa CBN ta ba da umarnin aiwatar da wani sabon salo na manufofinta da zai kai ‘yan Najeriya da biyan wasu caji ga bankuna don ajiyar kudi a asusun kowace banki.

2. Shugaba Buhari zai Bar Najeriya Ranar Lahadi Don halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya A Amurka

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a karshen wannan makon zuwa Amurka, don halartar taro na 74 na Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA74).

Naija News ta samu labari da tabbacin tafiyar shugaban ne a bakin Tolu Ogunlesi, Mataimakin sa na musamman kan rariya, a wata sanarwa da ya bayar a layin yanar gizon nishadi ta Twitter.

3. Najeriya Ta Nemi sabon Rancen Kudi $2.5bn daga Bankin Duniya

Shugabancin Najeriya ta nemi Bankin Duniya don bada rancen dala biliyan 2.5, in ji Hafez Ghanem, mataimakin shugaban bankin duniya na Afirka.

A yayin da yake magana yayin wata hira da aka yi a ranar Laraba a Abuja, Ghanem ya bayyana da cewa har yanzu cibiyoyar kudin na duniya suna kan tattaunawa da gwamnatin Najeriya game da rancen.

4. Ekiti: PDP Ta Kalubalanci Fayemi Domin Nadin Alkalin Kotu da aka kora a Matsayin Shugaban SIEC

Jam’iyyar PDP ta reshen jihar Ekiti, ta kalubalanci Kayode Fayemi don nada Mai shari’a Jide Aladejana da aka sallama a baya a matsayin shugaban Hukumar Zabe ta Jihar Ekiti.

Jam’iyyar adawar ta yi ikirarin cewa nadin Jide a matsayin zai haifar da wasu nauyi a kan hukumar zaben.

5. Biafra: Nnamdi Kanu ya bayyana Abinda ya tattauna da UN

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya bayyana da cewa ya gabatar da batutuwan da suka shafi mutanensa a gaban manyan kungiyoyi da hukumomin Majalisar Dinkin Duniya (UN).

Naija News ta samu tabbacin bayanin Nnamdi Kanu ne a wata rahoton da ya fitar ta hannun sakataren watsa labarai da sakataren kungiyar IPOB, Emma Powerful, ya bayar a ranar Alhamis, 19 ga Satumba.

6. Osinbajo ya jagoranci Taron Majalisar Tattalin Arzikin Kasa

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, A ranar Alhamis din da ta gabata ya jagoranci taron kwamitin tattalin arzikin kasar a fadar shugaban kasa, Abuja.

Naija News na da sanin cewa Mataimakin shugaban kasan, Osinbajo, bisa dokar da tsarin mulkin Najeriya, shine ke shugabancin Hukumar NEC.

7. Shugabannin Jam’iyyar PDP Sun Haɗu A Dubai Game Da Batun Karar Zaɓe

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya gana da mambobin kwamitin amintattu (BoT) na jam’iyyar game da hukuncin Kotun Shugaban kasa, ‘Petition Tribunal (PEPT)’.

Ka tuna da cewa Kotun sauraron karar shugaban kasa (PEPT) a ranar Laraba da ta gabata ta yi watsi da karar da PDP da dan takarar shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar, suka gabatar.

8. Muna Aiki Fiye da Ministoci, Mun Dace kuwa da Motar SUVs mai Tsadar Biliyan N5.5bn – Majalisar Dattawa

Jagoran Majalisar Dattawa, Yahaya Abdullahi ya yi Allah wadai da koke-koke da al’ummar kasa ke yi game da matakin babban zauren majalisar ta na kashe Naira biliyan 5.5 a kan sayan motoci da ‘yan Majalisar.

A cikin bayanin Yahaya yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke Abuja a ranar Laraba, Jagoran Majalisar Dattawan ya ce “cin mutunci ne ga jama’a da yin Allah wadai da matakin da ta yanke na kashe kudi kan siyan motoci”.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Nishadi: Umar M Sharif Ya Fito da Sabuwar Waka ‘SABADA’ tare da Korede Bello

Shahararran Mawaki, Dan Shirin Fim da kuma jigo a Kannywood, Umar M Sharif ya fitar da sabuwar waka mai taken ‘SABADA’, hade da shahararran Mawaki da dan tashe a Najeriya, Korede Bello.

Naija News Hausa ta samu tabbacin fitar wakar ne bisa wata sako da aka aika a layin yanar gizon Nishadi da Twitter a ranar 2 ga watan Satumba 2019 ta hannun Umar da kansa @OfficialMSharif.

Kalli Sanarwan a Kasa, bisa nan ga Wakar a nan Kasa:

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 20 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 20 ga Watan Agusta, 2019

1. Oyo-Ita ya kaurace da kasance hidimar Ilimantar da sabbin Sanatoci da Buhari ya jagoranta

Shugaban ma’aikatan kwadagon na tarayya, Winifred Oyo-Ita bata halarci taron Ilimantar da sabbin Ministoci wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta na shekarar 2019.

Naija News ta tuna da cewa Hukumar kare tattalin arzikin kasa da yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta tuhumi Oyo-Ita a makon da ya gabata kan zargin almundahana da rashawa na kudi N3b.

2. Kungiyar NASU, SSANU sun fara Yajin Aiki a dukan fadin Kasar Najeriya

Wakilan kungiyar Malaman Jami’o’in da ba sa koyarwa (NASU) da kuma Manyan Ma’aikata na Jami’o’in Najeriya (NASU) sun fara yajin aiki na kwanaki biyar.

Kwamitin Ayyuka na NASU da SSANU wadanda suka ba da umarnin yajin aikin sun bayyana cewa sun yi hakan ne bayan da Gwamnatin Tarayya ta kaurace da bin gargadin da aka basu da Korafin kwanaki 14.

3. Abin da Shugaba Buhari Ya gayawa sabbin Ministoci a Lokacin Jawabi

A ranar Litinin din da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da wa’adin shugaban kasa ga wadanda aka zaba ga kujerar ministoci, tare da sauran manyan ma’aikatun gwamnati.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa wannan hidimar anyi ta ne don kafada Ministocin da zasu yi aiki tare da Shugaban kasa nan da shekaru hudu masu zuwa, tare da tantance matsayin kasar a 2015 zuwa inda take a yau da kuma tsara hanya don ci gaban kasar nan gaba.

4. IPOB na Barazanar wulakanta Buhari da Buratai

Bayan harin da aka kaiwa tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ‘Yan asalin kasar Biafra, sun yi barazanar wulakanta Shugaba Muhammadu Buhari a duk lokacin da ya fita daga Najeriya zuwa kasar Turai.

Kungiyar a cikin sanarwar da ta fitar ta kuma yi barazanar cewa za ta wulakanta Shugaban Hafsun Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai.

5. Shugabancin APC na Liyafa cikin Cin Hanci da Rashawa – Timi Frank

Tsohon Mataimakin Kakakin yada Yawun Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Timi Frank, ya bayyana cewa akasarin ‘yan Najeriya suna ganin yadda jagorancin Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke rawa tsirara da liyafa cikin Cin Hanci da rashawa a gida da kuma na hadayyar kasa baki daya.

Wannan bayanin Mista Frank ya biyo ne bayan rahoton da Gwamnatin Amurka ta bayar wanda ya la’anci gwamnatin Buhari bisa ci gaba.

6. Gwamnatin Tarayya Ta Mayar da Martani game da Yin Jima’i a BBNaija

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fid da kara ga Hukumar Watsa Labarai da Nishadi ta Kasa (NBC) game da wasan kwaikwayon soyayya mai ban sha’awa da ake yi mai taken “Big Brother Naija”.

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta cimma matsaya tare da Startimes don gabatar da wani shiri da zai musanya BBNaija wanda zai yada da kuma karfafa al’adun kasar Najeriya.

7. Kotu ta dakatar da AGF, ICPC Daga Kwace kayan Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Yari

Tsohon Gwamnan jihar Zamfara, Abdulazeez Yari ya samu nasarar umarnin Kotu ta kiyaye shi daga cin hanci da rashawa da kuma wasu kungiyoyi masu alaka da shi (ICPC).

Naija News ta tuna cewa a a baya Bankin Gwamnan da ke a Polaris da bankin Zenith sun karbi izinin kotu na rufe Asusun Gwamnan bayan da wata rukunin hukumar tsaro ta (EFCC) ta hari gidansa da bincike a makon da ta gabata.

8. Gobara ta lalata kasuwar Katangowa A Legas

Gobarar ta Barke a wani sanannen kasuwar da ake kira Katangowa inda a ke sayar da tsohin kayaki a karamar hukumar Agbado / Okeodo a nan jihar Legas, a kan hanyar Legas-Abeokuta Expressway.

Naija News ta fahimci cewa barkewar gobarar da ta fara da misalin karfe 3.15 na safiya ta lalata tsawan wasu shagunan suttura da ke a cikin kasuwar a gaban babban masallacin Juma’a na kasuwar.

Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Kannywood: Anyaka wa fitacen jarumi dan Shirin Fim kafa don Tsanancin Ciwon Daji

Abin takaici, Naija News Hausa ta samu sanin cewa anyankewa fitatcen Jarumin kannywood, Sani Idris MODA kafa sanadiyyar matsanacin ciwon daji da yake fama dashi na tsawon lokatai.

Sanarwan ya bayyana ne a layin yanar gizon nishadi ta Twitter wadda Musa Kutama [@kutamamuhammad] ya bayar.

Ga sakon a kasa karmar haka;

Innalillahi Wainna ilaihiraju’un anyankewa fitatcen Jarumin kannywood Sani Idris MODA kafa sanadiyyar matsanacin ciwon daji da yake Fama dashi.
Majiyar mu ta bayyana mana cewa anyi aikin cikin nasara yanzu haka yana kara samun sauki.
Muna rokon Allah ya kara masa lafiya #Ameen

Kalli Bidiyon lokacin da Ali Nuhu ya ziyarceshi a kan gadon asibiti;

https://www.youtube.com/watch?v=OUSDMdqej7I

Ka tuna da cewa Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Ali ArtWork da aka fi sani da ‘Madagwal,’ Na cikin Mawuyacin yanayin rashin lafiya.

Ko da shike dai a baya an iya gane da cewa sauki ya samu ga shahararran.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 4 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 4 ga Watan Yuli, 2019

1. A karshe Shugaba Buhari ya janye zancen kafa Ruga a Jihohin Najeriya

A ranar Laraba da ta wuce, Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta janye shirin kafa Ruga a Jihohin kasar kamar yadda aka gabatar a baya ga rahotannai.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya dauki wannan matakin dakatar da kafa Ruga ne bayan da al’umar Najeriya suka bayyana rashin amincewarsu da hidimar.

2. Kotun Tribunal ta hana PDP mayar da martani ga wata zancen APC

Kotun hukunci ga shugabancin kasa da ke a birnin Abuja tayi watsi da bukatar Jam’iyyar Dimokradiyya da dan takaran su ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019, Atiku Abubakar, da neman yancin mayar da martani ga wata bukatar da APC tayi ga kotun.

Naija News ta gane da cewa Jam’iyyar PDP ta Atiku, a baya ta kauracewa wa wata zance da Jam’iyyar APC ta gabatar tun ranar 10 ga watan Yuni, 2019 da ta gabata.

3. Shugaba Buhari ya amince da rattaba hannu ga hidimar AFCFTA

A karshe, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana amincewa da rattaba hannu ga hidimar Yankin fannin cinikayyar nahiyar Afirka (AfCFTA), a karshen wannan mako.

Naija News ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a layin yanar gizon nishadi ta Twitter @NGRpresident, ranar Laraba da ta gabata.

4. Osinbajo da Gwamnonin Jiha sun yi wata ganawan Kofa kulle

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Laraba da ta wuce, ya gana da gwamnonin Jiha a cikin Aso Rock.

Ko da shike ba a sanar da dalilin ganawar ba, amma Naija News Hausa na tuhumar cewa watakila sun yi zaman tattaunawar ne akan zancen dakatar ko kuma kafa Ruga a Jihohin kasar.

5. Ma’aikatan Maritime sun fara Yajin Aiki

Hukumar Ma’aikatan Maritime ta Najeriya (MWUN), ta dakatar da aiki a dukan rukunin aikin su a kasar, ta kuma gabatar da yajin aiki ga dukan ma’aikatan su.

Naija News Hausa ta gane da cewa hukumar ta dauki matakin ne bayan da ta bayar da tsawon kwanaki 14 ga Gwamnatin Tarayyya da umurtan Kamfanonin kasa da biyan albashin ma’aikatansu da kuma magance wasu matsaloli da ya kamata.

6. Gbajabiamila ya kauracewa zabin da PDP tayi na jagoran karamar Majalisa

Kakakin yada yawun Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, ya sanar da Ndudi Elumelu a matsayin jagoran karamar rukunin majalisar wakilai.

Naija News ta fahimta cewa Femi ya gabatar da Elumelu da kauracewa zabin Jam’iyyar PDP da ta bada sunan Kingsley Chinda a matsayin jagoran karamar rukunin majalisar.

7. Sanata Elisha Abbo ya zalunci wata mata a birnin Abuja

Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilci a Arewacin Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) ya zalunci wata Macce da kwakwada mata mari cikin wata shago, inda ake sayar da kayan yin Jima’i a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta gane da cewa Sanata Abbo ne sanata mai kanancin shekaru a cikin Sanatocin Najeriya.

8. Atiku da Jam’iyyar PDP zasu fara gabatar da shaidu a yau

Jam’iyyar Dimokradiyyar da Dan takaran kujerar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar na a shirye don fara gabatar da shaidun tabbacin nasarar sa ga Buhari a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da ta wuce.

Naija News ta gane da cewa Atiku da PDP sun sanar a baya da cewa zasu gabatar da hakan a yau, Alhamis, 4 ga watann Yuli.

9. Sanata Elisha Abbo ya roki Matar da ya zalunta

Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Adamawa a ranar Laraba da ta wuce yayi wata gabatarwa akan bidiyon da yada ya zalunci wata mata a Abuja, da ya riga da mamaye layin yanar gizo.

A bayanin Sanata Abbo a ranar Laraba, ya roki ‘yan Najeriya, Jam’iyyar PDP, Majalisar Dattijai, Iyalinsa da Matar da ya zalunta da su gafarce shi da laifin da ya aikata.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Ga sabuwa: Shugaba Buhari ya dakatar da zancen kafa RUGA a Jihohin Kasar Najeriya

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta janye da dakatar da shirin kafa #RUGA a Jihohin kasar kamar yadda aka gabatar a baya a rahotannai.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya dauki wannan matakin dakatar da kafa #RUGA ne bayan da al’umar Najeriya suka bayyana rashin amincewarsu da hidimar.

Ka tuna a baya da cewa Kungiyar zamantakewa da ci gaban Al’umma Iyamirai da aka fi sani da Ohanaeze Ndigbo, sun dage da cewa ba zasu bayar da fili ga makiyaya Fulani ba don kiwo a Kudu maso gabashin kasar.

Haka kazalika mazaunan yankin Nnewi, a Jihar Anambra suka kori wasu makiyaya Fulani daga garin su a tsakar rana, a cikin wata bidiyo da Naija News Hausa ta ci karo da shi a layin yanar gizon nishadi.

Cikakken bayani game da matakin shugaba Buhari a kan dakatar da kafa #RUGA zai biyo daga baya.