Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 4 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 4 ga Watan Yuli, 2019
1. A karshe Shugaba Buhari ya janye zancen kafa Ruga a Jihohin Najeriya
A ranar Laraba da ta wuce, Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta janye shirin kafa Ruga a Jihohin kasar kamar yadda aka gabatar a baya ga rahotannai.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya dauki wannan matakin dakatar da kafa Ruga ne bayan da al’umar Najeriya suka bayyana rashin amincewarsu da hidimar.
2. Kotun Tribunal ta hana PDP mayar da martani ga wata zancen APC
Kotun hukunci ga shugabancin kasa da ke a birnin Abuja tayi watsi da bukatar Jam’iyyar Dimokradiyya da dan takaran su ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019, Atiku Abubakar, da neman yancin mayar da martani ga wata bukatar da APC tayi ga kotun.
Naija News ta gane da cewa Jam’iyyar PDP ta Atiku, a baya ta kauracewa wa wata zance da Jam’iyyar APC ta gabatar tun ranar 10 ga watan Yuni, 2019 da ta gabata.
3. Shugaba Buhari ya amince da rattaba hannu ga hidimar AFCFTA
A karshe, shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana amincewa da rattaba hannu ga hidimar Yankin fannin cinikayyar nahiyar Afirka (AfCFTA), a karshen wannan mako.
Naija News ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a layin yanar gizon nishadi ta Twitter @NGRpresident, ranar Laraba da ta gabata.
4. Osinbajo da Gwamnonin Jiha sun yi wata ganawan Kofa kulle
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Laraba da ta wuce, ya gana da gwamnonin Jiha a cikin Aso Rock.
Ko da shike ba a sanar da dalilin ganawar ba, amma Naija News Hausa na tuhumar cewa watakila sun yi zaman tattaunawar ne akan zancen dakatar ko kuma kafa Ruga a Jihohin kasar.
5. Ma’aikatan Maritime sun fara Yajin Aiki
Hukumar Ma’aikatan Maritime ta Najeriya (MWUN), ta dakatar da aiki a dukan rukunin aikin su a kasar, ta kuma gabatar da yajin aiki ga dukan ma’aikatan su.
Naija News Hausa ta gane da cewa hukumar ta dauki matakin ne bayan da ta bayar da tsawon kwanaki 14 ga Gwamnatin Tarayyya da umurtan Kamfanonin kasa da biyan albashin ma’aikatansu da kuma magance wasu matsaloli da ya kamata.
6. Gbajabiamila ya kauracewa zabin da PDP tayi na jagoran karamar Majalisa
Kakakin yada yawun Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, ya sanar da Ndudi Elumelu a matsayin jagoran karamar rukunin majalisar wakilai.
Naija News ta fahimta cewa Femi ya gabatar da Elumelu da kauracewa zabin Jam’iyyar PDP da ta bada sunan Kingsley Chinda a matsayin jagoran karamar rukunin majalisar.
7. Sanata Elisha Abbo ya zalunci wata mata a birnin Abuja
Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilci a Arewacin Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) ya zalunci wata Macce da kwakwada mata mari cikin wata shago, inda ake sayar da kayan yin Jima’i a birnin Abuja.
Naija News Hausa ta gane da cewa Sanata Abbo ne sanata mai kanancin shekaru a cikin Sanatocin Najeriya.
8. Atiku da Jam’iyyar PDP zasu fara gabatar da shaidu a yau
Jam’iyyar Dimokradiyyar da Dan takaran kujerar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar na a shirye don fara gabatar da shaidun tabbacin nasarar sa ga Buhari a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da ta wuce.
Naija News ta gane da cewa Atiku da PDP sun sanar a baya da cewa zasu gabatar da hakan a yau, Alhamis, 4 ga watann Yuli.
9. Sanata Elisha Abbo ya roki Matar da ya zalunta
Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Adamawa a ranar Laraba da ta wuce yayi wata gabatarwa akan bidiyon da yada ya zalunci wata mata a Abuja, da ya riga da mamaye layin yanar gizo.
A bayanin Sanata Abbo a ranar Laraba, ya roki ‘yan Najeriya, Jam’iyyar PDP, Majalisar Dattijai, Iyalinsa da Matar da ya zalunta da su gafarce shi da laifin da ya aikata.
Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com