Connect with us

Labaran Najeriya

Asha: Rikici ta barke a Majalisar Dattawa tsakanin Sanatoci Inyamurai na Arewa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rikici ya barke a Majalisar dattawan Najeriya a yau Talata, 11 ga watan Disamba lokacin da Sanatoci sukayi cacan baki kan tabbatar da sabbin mambobin Kungiya ta Binciken Kudi da Tattalin Arziki ta Kasa da suna (EFCC). Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen sabbin mambobin hukumar uku ga majalisar dattawa a watan Yulin 2016. Mambobin sune Ndasule Moses, Lawan Mamman, Galadanci Najib da Adeleke Adebayo Rafiu. Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan yakin da rashawa, Chukwuka Utazi, ya mika aikin kwamtinsa ga yan majalisa domin tabbatar da su.

Ana cikin magana sai Sanata Victor Umeh ya nuna bacin ransa kan wadanan da Shugaba Buhari ya nada saboda an nuna bangaranci a dukkan nade-naden da akayi a kwanakin nan, an mayar da yankin kudu maso gabas saniyar ware. Ya bayyana cewa yayinda shugaban EFCC, Ibrahim Magu dan arewa maso gabas ne, sakataren hukumar, Olanipkekun Olukoyede, dan yankin yarbawa ne kuma wadannan sabbin kuma yan arewa ne. Saboda haka, kada a tabbatar da sunayen har sai an sake duba wannan lamari. Wannan ya jawo cece-kuce cikin yan majalisan inda shugaban masu rinjaye, Ahmed Lawan, yace majalisar ta cigaba aikinta ta tabbatar da su, sanatocin yanki Igbo sunce sam ba za’ayi ba. Kawai sai yan majalisan suka rikita majalisar da zage-zage da hayaniya. Shugaban majalisar, Bukola Saraki, ya yi kokarin kwnatar da kuran amma ya gaza. Daga baya dole aka tashi daga zaman majalisa.