Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Gasan Maitamakin Shugaban Kasa ya nuna Atiku da maitaimakin sa ba u a shirye don shugabanci a 2019 – inji Bamidele

Published

on

at

Dan takaran Sanata na Jam’iyyar APC a jihar Ekiti, Hon Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa Dr Peter Obi bai iya bada isasshiyar manufa da kyakkyawan mafita ba kan hali da kasar mu Najeriya ke a ciki, ga gasar shugabanci da aka yi. wanna  ya nuna cewa basu a shirye don zaben shugaban kasa na  2019.

Bamidele ya ce abin takaici cewa PDP wanda ta zaburo don kawar da talaucin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta jawo, bata iya amfani da muhawara da gasar da aka yi ba don tabbatar da ‘yan Nijeriya cewa tana da mafita na musamman ga matsalolin da ke fuskantar kasar ba.

Ya ce bayyani da hanyoyin da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Obi ya lisafto wurin muhawarar watau a yankunan ilimi, tsaro, tattalin arziki, aikin noma da sauran su bai nuna cewa ‘yan Najeriya za su sami yarjejeniya mafi kyau fiye da yadda suke samu yanzu nan ba idan shugabansa, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben.

Tsohon Shugaban Majalisar wakilan ya yabawa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo don bada haske ga inda gwamnatin ta kasa wa yan Najeriya ga mulki da kuma bayyana cewa wannan abin takaici ne kawai ga kowane shugaba a Africa.

“A cikin tsaro, Obi ya yi alkawarin cewa za su karfafa sojojin Najeriya don su iya magance matsalolin tashin hankali a arewa maso gabashin kasar yayin da yake a bayyane cewa gwamnatin Buhari da Osinbajo ta zuba jari a bangaren tsaro fiye da kowace gwamnati.

“An ware kudi mai kimanin Naira Miliyan Dubu a shekara ta 2018 kawai, domin sayen kayan aiki don sojoji. kuma wannan ya sanya gagarumar nasarar da ake samu wajen yaki da Boko Haram.

“Jam’iyyar PDP ta kuma yi alkawarin ba da zaman lafiya ga ‘yan matalautan Najeriya , a lokacin da  wannan ke bayyane ga kowa cewa sama da mutane miliyan biyar suna jin dadin zaman lafiya a karkashin jagorancin APC a cikin tsarin N-Power, Matasa a aikin noma da ciniki da tsarin Tradermoni; wannan na daban kuma da wata shiri abinci a kyauta, wanda mulki Buhari ta jagoranta a makarantun duka.Advertisement
close button