Labaran Najeriya
Ba ni ne sanadiyar faduwar ka ba – Jonathan ya gayawa Buhari
Ka nemi wani asali amma bani ba ne sanadiyar kasawar ka ba
Abin mamaki ne cewa har yanzu shugaban kasar na neman wanda zai aza wa zargi akan kasawan sa a mulki, bayan shekaru uku da shigan sa a ofishin. in ji Jonathan. Tsohon shugaban ya fadi wannan ne ta hanyar sanarwar da kakakinsa, Mr Ikechukwu Eze, ya yi a Abuja a ranar Litinin.
Bayyanin na kamar haka, “Abin da haske kamar yadduwar rana: Gwamnatin Jonathan ba ta da wani sanadiya ga wannan shugabanci, tsarin ministoci ba daga shugaban da ke sauka ya kan fito ba.
Eze ya ce Jonathan ya yi kokarin kafa ƙungiyar tsara takardar sauka da ga mulki wanda ya samar da littafin ga Buhari kafin a ransar da shi.
Naija News ta ruwaito A ranar Litinin da Shugaba Muhammadu Buhari ke murnar ranar haihuwan sa na shekara 76 a garin Abuja, ya roki yan Najeriya su gane, su kuma fahimci manufarsa, a ba shi karin lokatai kadan da nan, a kuma ci gaba da taya shi da gwamnatin sa da addu’a.