Labaran Najeriya
Ka koma Daura ka huta – PDP sun gayawa Buhari
Jam’iyyar PDP sun ce wa Shugaba Muhammadu Buhari ya koma gidansa a Daura
Jam’iyyar PDP sun shawarci Buhari ya koma gidan sa a Daura yaje ya huta. sun fadi wannan ne wurin amsa wa rokon Shugaba Muhammadu Buhari inda yace yan Najeriya su bashi lokaci kadan. sun ce ba za a ba da shugabancin kasar nan ba ga mutumin da kullum a na neman ya huta, ya kuma yi barci dakyau.
Sakataren Harkokin Jakadanci, Mista Kola Ologbondiyan, ya gaya wa wakilinmu cewa shugaban ya koma gidansa a Daura, Jihar Katsina, inda ya ce ya, ya kamata Shugaba Buhari ya je ya huta.
Ya ce, bamu da wani lokaci da zamu watsar kuma. Kasar ba za ta bada dama ga Shugaba mai barci ba. Shugaba Buhari ya rigaya ya yi iyakar kokarin sa, amma kokarin na sa ya zam da kasawa ga bukatar kasar.
“Ya fada wa ‘yan Najeriya shekaru hudu da suka wuce cewa tsufa zai raunana kuzarin sa. kuma tabbas yana karuwa da tsufa a ko yaushe. Haka kuma Shugaban ya bayyana cewa likitocinsa sun ce ma sa ya huta, ya ci abinci, kuma ya yi barci sosai.
Ganin wadanan bukatu duka, ya kamata mu gaya masa gaskiya cewa kasar bata da bukatan jagoranci ga mutumin da ke da wadanan illa a wannan hali da kasar ke ciki.
“Muna da yawancin matasa zube da ba su da wata aikin yi, ‘yan ƙasa da sojoji na rasa rayukan su kullum ga yan ta’ada, hanyoyi basu da kyau ko kadan, tattalin arziki bai daidaita ba kuma duk da haka shugaban da aka ce ya huta na rokon a kara masa lokaci. shin, a kara masa lokaci na me?” Ologbondiyan ya ce a matsayin uba, shugaban ya bukaci ya koma gida ya huta.
Naija News ta ruwaito Wakilin wakilai na wakilcin Kazaure/Geisel/Yankwashi a Jihar Jigawa, Mohammed Kazaure, ya lura cewa Buhari Tsoho ne, amma ba wanda zai Rinjaye shi a shekarar 2019