Labaran Nishadi
Takaitaccen Tarihin Ali Muhammad Idris da aka fi sani da Ali Artwork
Tarihin shahararen dan wasa kwakwayo na Kannywood, Akta da Edita kuma
Dan matashin mai suna Ali Muhammad Idris da aka fi sani da Ali Artwork, an haife shi ne kuma ya girma ne Jihar Kano, a Yankin Tarauni ta Jihar Kano.
Kamar yadda na san kuna muradi na so gane ko shi dan shekara nawa ne
An haife Ali Muhammad Idris ne a ranar 1 ga Watan Janairu, a shekara ta 1992.
Ya fara makarantar firamare ne a wata Makaranta mai Suna Unguwan Uku Firamare Sukul a shekara ta 1999 zuwa shekara ta 2005. ya karasa da karatun sa a Makarantar sakandare farko watau (JSS 1) a Wata Makarantar sakandare ta gwamnati daga shekara ta 2005 zuwa 2008, bayan kammala wannan ya samu dace da ci gaba da karatun sakandaren a wata sakandare na Kundila, watau GSS Kundila daga Shekara ta 2008 zuwa 2011.
Daga nan ya haura zuwa Sa’adu Rimi College of Education Kumbotso a garin Kano, inda yayi karatun sa na NCE. ya Karanci Turanci/Hausa watau (English Language/Hausa, abin kaito bai iya ya kamala wannan karatun ba don matsalar kudi, ya dakatar da karatun sa daga Kalejin ne a NCE2.
Da yaga harkan samun kudi dan kamala karatun nasa ya zama da wuya sai ya shiga harkan kasuwancin daban daban kamar, aikin Tella, Jaye-Jaye hotuna, Edita na wasa, Wasan Fim, Kamedi da sauransu.
Da yaga ya kware kwarai da gaske ga wadannan ayuka a musanman aikin Edita na Fim wanda ya koya daga wani Ogan sa mai suna Aminu Mu’azu wanda aka fi sani da suna Aminu Bacci, sai dada ya fada wa aikin Edita shiga daya.
Naija News ta ruwaito Alhaji Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na shekarar 2019, ya fada da cewa idan har nuna masa so kuma aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya a 2019, zai tabbatar da ganin cewa bai manta da bangaren nishadi na Najeriya ba.
Daukan wannan mataki ya jawo wa rayuwansa tafarki mai kyau da ci gaba ta musanman har ma ya zama daya daga cikin sharararun Edita, Dan wasan kwaikwayo da Kamedi da ake ji da su a yau a hilin Kannywood da shirin Nishadi ta Hausa gaba daya.
Yayi aikin Shiri da Edita da shahararun yan wasa da kuma shirin fim, kamar Sani Rainbow, Ali Nuhu, Adam A. Zango, Aminu Saira, Abba Miko Yakasai, Usman Mu’azu, Naziru Dan Hajiya da sauransu.
Yayi aikin Edita na Fina-finai kamar su Maja, Gwaska, Ga mai ga doki, Duniya Makaranta, Soyayya da Shakuwa, Bayan Rai, Raddi, Ina mafita, Ashabul khafi, Birnin Masoya da sauransu.
Kalla kuma Musha Dariya Aliartwork Sabon Comedy 2018 – Arewa Comedians