Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Litinin 24, ga Watan Shabiyu, a Shakara ta 2018

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litinin, 24 ga Watan Shabiyu, 2018

1. Nnamdi Kanu ya zargi ‘masu yada labarai da boye gaskiyar mutuwar Buhari

Shugaban ‘yan kungiyar Biafra, Nnamdi Kanu ya zargi ‘yan yada labarai da cewa su ne sanadiyar wahalar da mutane ke fama da ita a kasan nan.

Ayayin da yake gabatarwar sa dan radiyo game da Jubril na Sudan a ranan Asabar da ta gabata, ya kara da tabbatar da cewa lallai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu da dadewa, cewa mutumin da ke Aso Rock ba Buhari bane. Ya zargi masu yada labarai da boye wannan gaskiyar.

2. Gwamnatin tarayya bata dauki shirin dakatar da Yajin aiki da muhimanci ba – Kungiyar ASUU

Shugaban Jami’ar ‘yan ASUU na Jihar Calabar, Dokta Tony Eyang ya ce yana da shakkar Gwamnatin Tarayya ga nuna muhimanci ga dakatar da Yanjin aiki da ake ciki.

A cewar Eyang, mataki daya kawai gwamnatin tarayya za ta yi don nuna alƙawari kullawa da yajin aikin, matakin kuwa shi ne su cika daya daga cikin alkawuran da su ka yi wa kungiyar.

3. Jam’iyyar APC za ta kasance mafi rinjaye a majalisar dattijan bayan zaben 2019 – inji Lawan

Sanata Ahmed Lawan, Sanata mai wakiltar Jihar Arewa ta Yobe ya yi ikirarin cewa za yan Jam’iyyar APC za ta mamaye Majalisar Dattijai bayan zaben 2019.

Sanatan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Jihar Bauchi yayin da yake magana da manema labarai bayan suk karshe zaman Kungiyarsu.

4. Atiku faras ma Shugaba Buhari game da kasafin shekarar 2019

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya faras ma shugaba Muhammadu Buhari a kan kasafin kudin 2019 da aka gabatar a majalisar dokokin kasar makon da ya wuce.

Atiku ya ce, kasafin kudin bai da wata mafita ga halin da ake ciki a kasar yan zun nan.

5. Gwamnatin Jihar Akwa Ibom za ta hana Buhari amfani da filin wasan kwallon su don Kampen

Gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi amfani da Godswill Akpabio International Stadium, Uyo ba, don shirin zaben sa na shekarar 2019 wanda yake shirin yi ranar Jumma’a na gaba.

Jihar ta yadda ne Shugaban yayi anfanin da wata Fili maimakon Babbar Filin da shugaban ya bukata, duk da cewa filin ba zai dauki yawan mutane ba kamar babbar filin.

6. Nnamdi Kanu na barazanar tashin hankali idan aka sake zabar Ikbizu  a Jihar Abia

Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ‘yan Biafra (IPOB), ya ce Abia za ta “kama da wuta” idan har an sake zaban Gwamna Okezie Ikbizu a matsayin gwamnan jihar a zaben 2019.

Ikpeazu, wanda aka zabe shi a matsayin gwamnan Jihar Abia a shekara ta 2015 na neman shiga mulki karo na biyu a karkashin Jam’iyyar PDP.

7. Ba za mu yi musayar kalamai ba da ‘yan majalisa a kan kasafin kudi ta shekara 2019

Ministan watsa labarai, Lai Muhammad, ya bayyana cewa shugabancin ba ta da lokaci don musayar kalamai da yan majalisa.

Ya fadi wannan ne sanadiyar maganar da shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya yi a kan kasafin kudi ta shekarar 2019.

8. Jam’iyyar APC ta yi musun bayyyanar Kangi a shugabancin Buhari

Majalisun Jam’iyyar APC ta ƙaryata zargin cewa wata Kangi a Aso Rock tayi kulle da kampen na Shugab Muhammadu Buhari.

Rahoto ta bayar cewa wata kangi ta kame shirin kampen damu cewa sun yi wata shirin don dakatar da wasu mambobi na Jam’iyyar ga ayuka.

9. Buhari zai yi hukumta wadanda suka masa tsuwa a yayin da yake gabatar da kasafin kudi a Majalisa – Fani Kayode

Tsohon Ministan zirga-zirga, Femi Fani Kayode ya bayyana shirin Shugaba Muhammadu Buhari ga wadanda suka yi masa tsuwa a yayin da yake gabatar da kasafin kudi a makon da ta gabata.

Tsohon Minista ya ce wata majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana masa cewa shugaban ya yi rantsuwa da cewa lallai zai hukumta yan Majalisar da suka aiwatar da wannan hali.

10. Oshiomhole mai surutai ne kawai  – Okorocha

Gwamna Rochas Okorocha ya bayyana shugaban ‘yan Majalisar APC, Adams Oshiomhole a matsayin ma suruci ne kawai.

Okorocha ya kara da cewa Oshiomhole a matsayin sa na tsohon gwamnan jihar Edo, na da bashin albashin ma’aikata na tsawon watannai bakwai da bai biya ba a lokacin da ya bar ofishin.

 

Sami karin labarai ta Najeriya a www.hausa.naijanews.com