Connect with us

Labaran Najeriya

IPOB: Nnamdi Kanu zai bada tabbatacen shaida na cewa ba Buhari ne ke Aso Rock

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban Kungiyar ‘Yan Biafra, Nnamdi Kanu zai yi gabatarwa daga kasan Israila

Mazi Nnamdi Kanu, sananen shugaban yan Biafra ya yi alkawarin gabatar da tabbatacen shaida da zai bawa al’umma gaba daya mammaki a ranar Sati 22, ga Watan Disamba 2018 daga kasan Israila don tabbatar masu da cewa ba Muhammadu Buhari ne kan mulki ba, an rigaya an musanya shi da wani.

Kungiyar IPOB din  a wata sanarwa daga bakin kakakin kungiyar, Emma Powerful ta ce, za ta bayyana ga jama’a tabbatacen shaida da cewa an musanya Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da wani mai suna Jubril daga Sudan.

Sun kuma bayyana a mayadun labarai in da yan Najeriya duka da mai son ji zai ji wannan gabatarwa na shedar cewa ba Buhari ne ke a mulki ba.

Naija News ta ruwaito cewa Nnamdi Kanu ya fada kwanakin baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya mutu ko kuma an musanya shi da wani daga kasar Sudan da ake ce da shi Jubril .

Ko da shi ke, Shugaban Kasan ya fito a fili a yayi musu da wannan zargin, cewa karya ne, shi bai mutu ba, ba kuma yi musayan sa ba ko kuma kira wata jiki mai kama da shi. Buhari ya fadi wannan ne lokacin da ya je kasan Poland.

Lokacin da za ayi wannan gabatarwa:
* 6:00 PM Biafra Time ( Lokacin Najeriya)
* 5:00 PM London Time
* 7:00 PM Berlin Time
* 8:00 PM Jerusalem, Israel Time
* 7:00 PM Paris, France Time.
* 2:00 AM Tokyo, Japan Time.
* 7:00 PM South Africa Time.
* 7:00 PM Rome, Italy Time.
* 10:30 PM India Time.
* 8:00 PM Cyprus Time.
* 1:00 PM Washington, DC, USA Time.
* 8:00 PM Nairobi, Kenya Time.
* 2:00 AM Tokyo, Japan Time.
* 7:00 PM Berlin, Germany Time.
* 8:00 PM Moscow, Russian Time.
* 2:00 PM Brazilian Time.
* 7:00 PM Madrid, Spain Time.

Muna gayyatar yan Najeriya duka su kasa kunne ga Radiyon su don jin wannan labari dadai lokacin da aka sanya.

Karanta kuma Dalilin da ya sa Mutumin da ke Aso Rock ba Buhari bane da muka zaba’ – Bolaji Abdullahi

Sami cikakkun labarai a Naija News Hausa