Connect with us

Uncategorized

Asha: Jirgin Sojojin Sama da ke taimakawa ga yakin Boko Haram ta fadi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jirgin sama  ta Sojojin yakin sama na Najeriya (NAF) da ke kai taimako ga rundunar soji na Bataliya 145 a Damasak a Arewacin Jihar Borno ta fashe a ranar jiya, Laraba 2, ga watan Janairu, da dare.

Air Commodore Ibikunle Daramola, Daraktan Harkokin Sanarwan rundunar ne ya bada wannan rahoto a jiya laraba.

Duk da cewa Daramola bai bayyana irin jirgin ba da ta fashe, ko kuma yawan mutane da ke a cikin ta a lokacin da ta fashe. Rundunar dai ta Sojojin sama ta Najeriya na da fiye da dozin na jiragen sama da aka farasa daga kasar Russhia, kamar su MMil Mi-17 da kuma Mil Mi-24.

Daramola ya ce, wannan lamarin ya faru ne shiyoyin karfe 7:45 na dare a yau biyu 2, ga watan Janairu 2019. “babbu tabbacin abin da ya kawo wannan fashewar jirgin har yanzu” in ji Shi.

“Da zarar an sami cikakken bayani game da hadarin, za a bayar ga jama’a duka,” in ji Daramola.

Sami kari labarai a Naija News Hausa