Connect with us

Uncategorized

Hukumar INEC ta fito da Fom na karban Mallaman gudanar da aikin zaben 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar INEC ta gabatar da shirin daukar malaman da zasu gudanar da shirin zaben 2019

‘Yan kwanaki kadan da zaben tarayya da za a fara watan Fabairu mai zuwa, Hukumar gudanar da shirin zabe, INEC sun fito da fom don daukar mallaman zabe, wadanda za su aiwatar da ayukan zaben idan lokaci ya yi.

Kamar yadda muka sami rahoto da tabbacin wannan a yau Talata 15 ga watan Janairu, 2019, tsarin daukar na kamar haka:

1. Supervisory Presiding Officer  – (SPO)
2. Registration Area Center  – (RAC) Manager
3. Presiding Officer – (PO)
4. Assistant Presiding Officer – (APO)
5. Registration Area Technical Support  – (RATECH)

Ana bukatar duk wanda ke so, ko bukatar cika wanna fom ya jefa sunansa da takardun sa a yanar gizon hukumar don samun wannan daman.

Za ka iya samun layin yanar gizon Hukumar Anan: INEC

Allah ya sa ka dace, Amin.