Connect with us

Uncategorized

Kada ku Tsorata don cutar ‘Lassa Fever’ – Dokta Chikwe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun sanar a Naija News kwanakin baya da cewa rundunar sojojin Najeriya sun yi tugumar cewa mugun cutar ‘Lassa Fever’ ne ya kama wani sojan su da ya mutu bayan rashin lafiyar ‘yan kwana kadan da dawowar shi daga juyayin tsohon sa da ya rasu a Jihar Kogi.

A yau Laraba, 23 ga Watan Janairu, 2019, Hukumar Kulawa da Cututtuka Kasar Najeriya (NCDC) sun fada da cewa kada ‘yan Najeriya su tsorata da kamuwar cutar, don sun rigaya sun samar da matakai don magance yaduwar cutar a kasa.

Wannan shi ne fadin Shugaban Hukumar (NCDC), mai suna Dokta Chikwe Ihekweazu a birnin Abuja a yau Laraba.

Ya ce “Hukumar NCDC na daukar matakai don magance duk wata ciwo ko cuta da za ta taso a wannan shekarar a kasar Najeriya”

“Mun kafa rukuni da dama don yaki da wannan, daya daga cikin su itace RRTs, wannan zasu hada gwuiwa da Jihohi don tabbatar da yaki da magance duk wata cuta mai taso wa ko da ke yaduwa” in ji Chikwe.

In ji shi, bincike ta nuna da cewa cutar ‘Lassa Fever’ kan taso ne lokacin rani tsakanin watan Janairu da watan Hudu na shekara.

Dokta Ihekweazu, ya bada shawara ga jama’a da cewa su yi ta kokarin cin abinci mai gina jiki da wadda ta dace da lafiyar jikunan mu duka, da kuma gyara wuraren zaman mu da ganin cewa kullum yana fes-fes.

“Ku kuma tabbata da cewa ku ajiye kayan gona da abin ci wuri mai kyau inda wata kwaro ko daba mai cuta ba zai iya kai ga abincin ba ko ga kayan gonar ba, don kare lafiyar jiki”.

“A tabbatar da cewa an wanke hannu da kyau kamin tsoma shi ga abinci, a kuma sha ruwa mai kyan gaske” in ji Doktan.

Ya kara da kira ga Gwamnatin Tarayya wajen taimakawa wa asibitocin yankuna da maguna da kayaki da zai taimaka ga yaki da cututtuka a kasar.

Chikwe ya kuma umurci mallaman kula da lafiyar al’umma da cewa su yi iya kokarin su wajen kadamar da ayukan su a hanya da ta dace, su kuma kasance da kula a kowace lokaci don yaki da cututtuka.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Sojojin Najeriya sun ba wa mutanen Natsinta da ke Jihar Katsina Magunguna don taimakawa da yaki da cututtuka a Yankin.

 

Kalla bidiyon: Yaki da Cutar Lassa Fever