Connect with us

Uncategorized

2019: Ku kiyaye sanya kakin ku zuwa wajen jefa kuri’a – Rundunar Sojoji ta bada Umurni ga Sojoji

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Ganin ya saura ‘yan kwanaki kadan da gabatowar zaben tarayyar kasa na shekarar 2019, Rundunar Sojojin Najeriya ta bada umurni ga sojoji da cewa kada wanda ya sanya kakin sa idan har zai je wajen jefa kuri’a ga zaben tarayya da ta gabato.

Rundunar sun sake tunar da dokokin su akan zaben kasa ga sojoji duka don kiyaye karye doka ga zabe.

Dokokin na kamar haka, kamar yadda Rundunar suka aika a shafin nishadarwa na twitter;

Sun gabatar da cewa kowa na da daman ya jefa kuri’a, idan har baya kan tsaro a lokacin, ko kuma a ranar.

Duk da cewa Sojojin na da daman yin zabe, ba a bada dama ba da zuwa wajen jefa kuri’a da kakin aiki, duk wanda ya yi wannan, lallai ya karya dokar rundunar akan lamarin zaben kasa.

“Ba daidai ba ne sojoji su nuna zabin su, ko ra’ayin su” inji rundunar. Dole ne ku kasance a tsaka, a matsayin ku na jami’an tsaro.