Connect with us

Labaran Najeriya

Karya ne, Buhari bai da shirin mayar da Najeriya kasar Musulunci – Inji Osinbajo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya mayar da martani ga zancen jita-jita da ake yi game da cewa Shugaba Muhammadu Buhari na shirin mayar da Najeriya a zaman kasar Musulunci.

“Na yi zama da kuma tattaunawa da shugaba Muhammadu Buhari, na kuma iya gane da cewa Buhari ba irin wannan mutumi ba ne, shi mai gaskiya ne da kuma fatan alhairi ga kasa”

“Buhari bai da wata shiri na mayar da kasar Najeriya a matsayin kasar musunlunci” inji Osinbajo a bayanin sa a Kurudu, nan Birnin Tarayyar kasa.

“Wannan jita-jita ba gaskiya bane,  duk shiri ce na makirci daga ‘yan adawa ganin cewa shugaba Muhammadu Buhari na samar da cin gaba a kasar” inji Osinbajo.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Farfesa Osinbajo ya bayyana cewa So ta gaske Buhari ke da shi ga kasar Najeriya.

Farfesa Yemi ya kara da cewa, “A cikin rukunin mu, muna da Kiristoci 20, Musulunmai 18 hade da wasu Manyan rukunin da suma Kiristoci ne” inji shi.

“Kai harma Boss Mustapha da ke matsayin babban sakataren Gwmanatin Tarayya, Kirista ne, shugaban kadamarwan mu ma Kirista ce, watau Mallam Winifred Oyo-Ita, saboda hakan ba yadda za a yi wannan zargi ga shugaban kasan da aikata da irin wannan shiri na musuluntar da kasar”.

Ya kara da cewa, haka kwanakin baya aka zargi Buhari a lokacin shugabancin Goodluck Jonathan da cewa Muhammadu Buhari ne ke goyawa wa ‘yan ta’addan baya.