Connect with us

Uncategorized

Ku zabi PDP don cin Nasara da Boko Haram – Atiku ya fada wa Mutanen Jihar Borno

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa Al’ummar Jihar Borno Alkawali tsaro.

A ranar Laraba, 6 ga Watan Fabrairu da ta gabata, Al’ummar Jihar Borno sun fito makil don marabtan dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a ziyarar hidimar yakin neman zabe da ya je a Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ya yi alkawali da cewa zai magance halin ta’addanci a kasar Najeriya, musanman a Jihar Zamfara.

Dan takaran ya fadi wannan ne a ziyarar hidimar neman zaben da ya je a Jihar Zamfara ‘yan kwanaki kadan da suka wuce.

A jiya Laraba, 6 ga Watan Fabrairu, Atiku Abubakar ya ziyarci Jihar Borno don kadamar da hidimar neman zaben sa ga shugabancin Najeriya a shekara ta 2019.

“Zaben Jam’iyyar PDP, zabe ce na yaki da ta’addancin Boko Haram  da kuma zamantakewa da kwanciyar hankali a Jihar Borno” inji Atiku.

Atiku ya kara da aikawa ga shafin nishadarwan sa na twitter bayan barin sa Jihar Borno. Ya ce “Na gode maku kwarai da gaske Jihar Borno State, duk da matsalar tsaro a Jihar, kun fito duk da iyalan ku don goyawa Jam’iyyar PDP baya”.

“A ranar 16 ga Watan Fabrairun, Ku fito duka don jefa kuri’ar ku. ku kasa, ku kuma tsare zaben ku” inji Atiku.

Ga hotunan yadda mutanen Jihar Borno suka marabci Atiku a Jihar Borno;

Karanta Wannan kuma: Wata Macce da ta tsage cikin ta da Reza a Jihar Bauchi don zafin na’uda.