Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Kali yadda jama’a suka fita ralin shugaba Buhari a Jihar Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar jiya Alhamis, 7 ga Watan Fabrairu, Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Adamawa don hidimar yakin neman sake zabe.

‘Yan kwanaki kadan ga zaben tarayya, Buhari ya ziyarci Jihar dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, mutanen Jihar Adamawa sun fito makil sun mamaye ko ta ina don nuna goyon bayan su ga shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019.

Muna da sani a da cewa Atiku Abubakar ya ziyarci Jihar Katsina a ranar jiya shi ma, inda rahoto ta bayar da cewa jama’ar Jihar Katsina sun fito kamar ruwan teku don bayyana goyon bayan su ga Atiku ga zabe na gaba.

Abin mamaki anan itace; Atiku ya samu marabtan mutane da yawa a Jihar shugaba Buhari, Katsina. Haka kuwa Shugaba Muhammadu Buhari ya samu goyon bayan jama’ar Jihar Adawa da yawan kwarai dagaske, watau garin Atiku dan takaran Jam’iyyar PDP.

Kalli hotunan ralin su da kanka ana;

Kalla a kasa kuma Ziyarar Atiku Abubakar a Jihar Katsina;