Uncategorized
Yadda za a Dangwala Yatsa ga takardan zabe
Akwai jita-jita da ya zagaya ga yanar gizo da cewa hukumar INEC sun canza yadda za a dangwala yatsa ga takardan zaben 2019.
Hukumar ta mayar da martani akan hakan da cewa ba gaskiya ba ne. Ana kokarin magance matsalar lalatar da takardan zabe ne kawai. An bukaci kowa ya yi amfani da yatsar Kashedi, watau yatsa ta biyu bayan babbar yatsan da ke hannun ka, ko a hannun ki.
Duk da hakan, ba dole ba ne amfani da yatsar, kana iya amfani da kowane yatsa, amma abin kula, kada wajen dangwala yatsa ga zabin ka, ka je ka dangwala wa wani can dabam. Ko kuma ka lallace takardan gaba daya da alli.
A kokarin magance wannan, Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta gabatar da yadda za a dangwala yatsa ga zaben tarayya da za a fara ranar Asabar, 16 ga Watan Fabrairun 2019.