Connect with us

Uncategorized

Jami’an Yan Sanda sun kame Masu Sace-Sacen Yara a Birnin Abuja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaron ‘Yan sandan Najeriya sun gabatar da kame wasu mutane uku da ake zargi da sace-sacen yara a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

“Mun kame barayin yara ukku da suka sace yara kanana biyu a nan gidan zaman birnin tarayya da ke a anguwar Karu, nan birnin Abuja” inji shugaban ‘yan sanda.

A bayanin kakakin yada yawun rukunin Jami’an tsaron ‘yan sandan yankin, DSP Anjuguri Manzah, “barayin yaran sun kadamar da batun sace yaran ne a ranar 11 ga Watan Fabrairu, 2019” inji DSP Manzah a bayanin sa da manema labarai a birnin Abuja.

“Bayan jin labarin bacewar yaran, sai muka aika jami’an tsaro a gaggauce don ganin cewa an kame wadanda suka aikata abin” inji Anjuguri.

Ya bayyana da cewa sun kame shugaban barayin ne a wajen da ta ke buya a nan wata kauyan Mararaba, ta Jihar Nasarawa a ranar 12 ga Watan Fabrairun. “Daga baya muka kuma kame sauran ‘yan kungiyar a anan Asokoro, cikin birnin Tarayya, Abuja a ranar Laraba, 13 ga Watan Fabrairu” inji shi.

“Mun riga mun mayar da yaran da aka sace ga Iyalan su”

Ya kara da cewa harwa yau ana kan bincike don wadannan barayin da kuma batun kai su gaban kotu.

DSP Anjuguri ya shawarci makarantu duka don zama da kulawa da kuma samar da tsaro a makarantu, musanman makarantun kananan yara don magance irin wannan.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Ministan yada Labaru da Al’adun kasa, Alhaji Lai Mohammed ya fada da cewa Leah Sharibu da ke kangin ‘yan ta’addan Boko Haram, bata mutu ba.