Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 14 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 14 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Dalilin rushewar Jirgin Farfesa Yemi Osinbajo a Jihar Kogi

Hukumar Bincike a kan Hadari (AIB) ta bayyana a yau, 14 ga Watan Fabrairu dalilin da yasa jirgin saman mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo ya fadi.

“Jirgin ta fadi ne don ta sauka akan yashi da filin da ke da yawar kura” inji babban shugaba da Kwamishinan hukumar (AIB), Akin Olateru.

2. AGF Malami ya bukaci hukumar INEC da dakatar da zaben Jihar Zamfara

Babban Mai Shari’a na Tarayya da Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya wallafa sako zuwa ga Hukumar zabe ta kasa (INEC) da bukatar hukumar ta dakatar da zaben gwamnoni, majalisai da zaben gidan wakilai a Jihar Zamfara don ba da dama ga Jam’iyyar APC da bayyana dan takaran su ga zaben.

An gabatar da Kwafi na wasikar mai shafi uku da Malami ya rattaba hannu da kuma bayar da hukumar ne a ranar 13 ga Fabrairu, 2019, watau ranar Alhamis.

3. Shugaba Buhari ya rattaba hannu ga takardar yarjejeniyar zaman lafiyar kasa

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar jiya, Laraba 13 ga Watan Fabrairu, ya kwatanta zaben bana a matsayin zabe mafi muhimanci ga ci gaban kasar Najeriya.

Shugaban ya fadi haka  ne bayan rattaba hannu ga takardan yarjejeniya ta zaman lafiyar kasar Najeriya a zaben shekara ta 2019.

4. Jam’iyyar PDP sunyi karar hukumar INEC akan Na’urar katin zabe

Jam’iyyar PDP ta gabatar da karar Hukumar zaben kasa (INEC) akan zargin yadda za a yi amfani da na’urar katin zabe ga zaben 2019.

A cikin takardan karar, Jam’iyyar PDP sun bukaci babban kotun tarayya na birnin Abuja,  da hana wa hukumar INEC zancen dakatar da zabe a wasu rumfunan zabe a sakamakon rashin aikain wasu na’urar bincika katin zabe.

5. Kotu ta bayar da belin Babachir Lawal, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya

Kotun Babban Birnin Tarayya, FCT a ranar Laraba da ya gabata, sun bayar da daman beli ga tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF, Babachir Lawal da wasu mutane biyu.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa Hukumar Bincike akan Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta kame Babachir Lawal ne a ranar Talata, 12 ga watan Fabrairun da ta gabata akan wata zargin da ake da shi na laifin cin hanci da rashawa.

6. Matsayi na bai dace da zubar Jinin kowa ba a kasar Najeriya – Inji Atiku

Dan takaran Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, a gabatarwan sa lokacin da ake hidimar rattaba hannu ga takardan zaman lafiyar kasa ga zaben shekarar 2019 da za a soma ranar Asabar, ya ce “Matsayi na bai dace da zubar Jinin kowa ba a kasar nan”

“Ina mai ba da gaskiya da kuma fatar cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi amfani da matsayin sa na shugabanci don ganin cewa zaben 2019 zai kasance da gaskiya ba tare da makirci ba”

7. Kotun CCT ta bada umarnin kame Alkali Walter Onnoghen (CJN)

Kotun CCT ta umurci hukumomin tsaro da tabbatar da kame Babban Shugaban Alkalan Shari’ar Najeriya da aka tsige a baya, Walter Onnoghen.

Danladi Umar, shugaban Kotun ne ya bayar da umurnin ga Jami’an ‘yan sanda da hukumar tsaro ta DSS don tabbatar da kama Onnoghen.

8. Yadda za a Dangwala Yatsa ga takardan zabe – Hukumar INEC

Akwai jita-jita da ya zagaya ga yanar gizo da cewa hukumar INEC sun canza yadda za a dangwala yatsa ga takardan zaben 2019.

Hukumar ta mayar da martani akan hakan da cewa, ba gaskiya ba ne. Ana kokarin magance matsalar lalatar da takardan zabe ne kawai. An bukaci kowa ya yi amfani da yatsar Kashedi, watau yatsa ta biyu bayan babbar yatsan da ke hannun ka, ko a hannun ki.

9. Yan Hari da bindiga da suka sace Ciyaman na hidimar zaben APC a Jihar Edo sun bukaci kudi Naira Miliyan N200m

Mahara da bindiga da suka sace Mista Monday Aigbobhahi, Shugaban Hidimar zabe na Jam’iyyar APC ga Lamarin Zaben Jihar Edo sun bukaci biyar kudi Naira Miliyan 200m kamin su sake shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun sace Mista Monday Aigbobhahi a Jihar Edo.

Ka sami cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa