Connect with us

Labaran Najeriya

Karanta abin da Sojoji suka ce game da zancen shugaba Muhammadu Buhari

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya sun yi alkawali da cewa zasu bi umarnin shugaba Muhammadu Buhari akan zancen da ya yi game da sace akwatin zabe.

Kamar yadda muka sanar a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya furta da cewa duk wani da ke shirin kwace akwatin zabe, yayi hakan ne don ranshi.

“Duk mai wata shiri na sace akwatin zabe, yayi hakan, amma yayi hakan ne a munsayar ransa” inji shugaba Buhari a cikin wata gabatarwa da yayi a ranar Litini da ta gabata.

Rundunar Sojojin sun bayyana da cewa dole ne idan shugaba yayi magana a kuma bi shi.

“Zamu ci mutuncin duk wanda ya dauki matakin sace akwatin zabe, kamar yadda shugaba Buhari ya bamu damar yin hakan a zaben 2019″ inji rundunar.

Ko da shike ‘yan Najeriya da dama sun furta da cewa wannan maganan bai da ba da shugaba Muhammadu Buhari. sun ce wannan furcin shugaban zai jawo kashe-kashe da zubar da jini ga zaben 2019.

“Idan har shugaba Muhammadu Buhari, babban Kwamandan Rundunar Sojojin kasar Najeriya zai bada irin wannan umarni, dole ne kuwa mi amince da shi kuma mu dauki matakai kamar yadda ya umurce mu da yi” inji kakakin yada yawun rundunar sojojin, Sagir Musa.

Mista Bola Tinu, babban shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, ya bayyana da cewa mutane da dama basu gane abin da shugaba Muhammadu Buhari ke nufi da bayanin sa ba.

“Dokar zaben kasa ta bayar da cewa duk wanda ya sace akwatin zabe ko wata kayan zabe, zai yi jarun shekara 2, amma ba wai a kashe shi ba” inji shi.

Karanta wannan kuma: ‘Yan Hari da makami sun kashe Boniface, Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Benue