Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari ya karyace zancen mayar da Najeriya kasar Islam

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Jumma’a, 22 ga Watan Fabrairu, shekara ta 2019, ‘yan awowi kadan da fara zaben shugaban kasa da ta gidan majalisa, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba baki ga zancen zargin cewa shugaban na da shiri na mayar da Najeriya kasar Islam.

“Kada ku musanya Siyasa da Addini” wannan shine kalmar shugaba Buhari a yayin da yake mayar da martani akan zargin.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa karya ce duk jita-jita da ake game da wannan batu na mayar da Najeriya a matsayin kasar Islam.

Mun sami bayyanin shugaban ne a Naija News ta wajen Mista Femi Adesina, Mai bada shawara ga shugaban kasa ta wajen yada labarai. “Kada ku musanya hidimar Siyasa da ta Addini” inji fadin sanarwan.

Sanarwan na kamar haka;

“Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya samu labari da sani da cewa wasu na zargi da jita-jita akan cewa yana da shirin mayar da kasar Najeriya a matsayin kasar Islam. Wannan zancen ba gaskiya bace ko kadan”.

“Wannan shiri ce na wasu don jawo kiyayya a kasa, musanman akan siyasa. sun kokarta da fadin hakan a shekara ta 2015 amma sun kasa ga cin nasara”

Shugaban ya ba da tabbaci da cewa yana a shirye da tabbatar cewa ya kare dokar kasan Najeriya kamar yadda ya yi rantsuwa a lokacin da ya hau mulkin kasar a shekara ta 2015.

“Wannan doka itace ta kare ra’ayin kowa a kasar da daman bautan a kowace addini da mutum ya gadama”

“Babu wanda zai tsananta kowa da bin wata addini da bai so da hakan ba. Kowa na da daman bin addini da ta yi masa” inji shugaba Buhari.

“Abu ne mai illa mutun ya musanya siyasa da addini” inji shi.