Connect with us

Labaran siyasa

APC/PDP: Ku guje wa ta’addanci, Sarki Sanusi Lamido ya gayawa ‘yan siyasan Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sarkin Jihar Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, yayi kira ga ‘yan siyasan Jihar Kano da cewa su guje wa halin ta’addanci a Jihar don zaman lafiyar kasa, musanman ga zaben 2019.

Sarkin ya fada da cewa abin takaici ne farmakin da ya faru tsakanin Jam’iyyar APC da Jam’iyyar PDP a Jihar a ranar Alhamis da ta gabata.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa ‘yan adawan Jam’iyyar APC sun tare Sanata Kwankwaso da mabiya bayansa a yayin da suke kan zagayan hidimar neman zabe a karamar hukumar Bebeji.

Sarki Sanusi ya bukaci hukumomin tsaro da su yi bincike ta musanman don ganin cewa sun kame wadanda suka aiwatar da wannan mugun farmakin, su kuma yi masu hukunci da ya dace akan doka.

Ya gabatar da hakan ne a yayin da yake bayani da manema labaran NAN a Jihar Kano yau Jumma’a, 22 ga watan Fabrairu.

Mun gane a Naija News Hausa kamar yadda muka sami rahoto, da cewa mutane biyu suka mutu a wajen farmakin, sa’anan kuma mutane da dama suka sami mugun raunuka.

Kakakin yada yawun hukumar ‘yan sandan Jihar, DSP Haruna Abdullahi, ya bayar ga manema labaran NAN da cewa motoci 20 aka kone, sa’anan kuma aka lallace wasu motoci 18 kuma. Ko da shike a baya mun ruwaito da cewa DSP Abdullahi ya bayyana da cewa ba zai tabbatar da kimanin mutane da suka mutu ba a wajen farmakin.

Karanta wannan kuma: Hukumar Jami’an ‘yan sandan Jihar Kwara sun kame Sanata Rafiu Ibrahim akan zargin kadamar da farmaki a Jihar.