Labaran Najeriya
‘Yan adawa sun kashe Chukwuemeka, mabiya bayan shugaba Muhammadu Buhari
Da ‘yan awowi kadan da fara zaben shugaban kasa da ta gidan majalisa, ‘yan hari da bindiga sun kashe wani mabiya bayan shugaba Muhammadu Buhari.
Mun samu rahoto a Naija News Hausa da cewa ‘yan hari da bindiga sun kashe Chukwuemeka Ishienyi, dan jam’iyyar APC da kuma kwararan mabiya bayan shugaba Muhammadu Buhari daga Jihar Enugu a Eha Alumona, karar hukumar Jihar.
Mun gane da cewa Chukwuemeka ne kawai ya saura ga uwarshi a matsayin da. kuma daman mamban Jam’iyyar PDP ne shi kamin ya shi da wasu mutane 1,000 suka koma jam’iyyar APC don goyawa shugaba Muhammadu Buhari baya a jihar.
Ko da shike da aka binciki kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Ebere Amaraizu, ya bayyana da cewa bai da wata cikakken bayani akan kisan a lokacin da ake karban wannan rahoto, amma ya tabbatar da cewa zai yi cikakken bincike akan hakan.
Mista Lawrence Alumona, Ciyaman na karamar hukumar Eha Uno a karkashin jam’iyyar APC, a wata bincike da manema labarai, yace “Ishienyi ya zo gida na kwanakin baya kamin a kashe shi, ya bayyana mani da cewa zai koma ga jam’iyyar APC, da cewa bai amince da yadda jam’iyyar PDP ke gudanar da al’amarin su ba”
“Jam’iyyar PDP suna ta barazanar cewa zasu ci mutunci na tun lokacin da na sanar da cewa zan janye daga jam’iyyar” inji bayyanin Ishienyi ga ciyaman na yankin kamin aka kashe shi.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa ‘Yan Hari da bindiga sun kashe wani ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Imo.
Mista Lawrence ya kara da cewa Jam’iyyar PDP sun kira Ishienyi ne don gane dalilin da yasa ya janye daga jam’iyyar, lokacin da yake kan hanyar dawowa daga wajen tattaunawar sai aka harbe shi” inji shi.
Karanta wannan kuma: Allah ne kawai zai iya dakatar da zaben ranar Asabar – inji Farfesa Mahmood