Connect with us

Uncategorized

Gobarar Wuta ya kame shaguna 200 a wata Kasuwa a Jihar Benue

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa akalla shaguna 200 suka kone kurmus a wata gobarar wuta da ya auku a babban kasuwar Makurdi Modern Market, a ranar Talata, 18 ga watan Yuni da ta wuce a Jihar Benue.

Bisa bayanin wani masana’anci a cikin kasuwar mai suna James Ekeson, ya bayyana ga manema labaran The Nation da cewa “gobarar wutan ya fara ne da maraicen ranar Talata a missalin karfe Shidda da rabi (6:30 pm), bayan da aka tashi cin kasuwar” inji shi.

Ko da shike James ya iya nuna da cewa “ba wanda har yanzu ya gane da sanadiyar gobarar wutan, a fadin shi kasuwar ta kulle ne tun karfe biyar da rabi na maraicen ranar, kuma babu wanda aka bari a ciki” inji Mista James.

Ya karshe da cewa kayaki da suka kone da lalacewa ga gobarar wutan ta sha karfin Miliyoyi.

Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa Gobarar Wuta ya kame shaguna Shidda a Kasuwar ‘Yan Rodi a Jihar Kano.

Ko da shike Kakakin yada yawun hukumar yaki da gobarar wuta na Jihar Kano, Malam Saidu Mohammed, ya bada haske da cewa ba wanda yayi rauni ga gobarar wutan, amma dai an yi rashin kayaki da dama.

Mista Saidu ya gargadi masana’anta da zama da kula da kuma yin hankali da duk wata abin da zai iya jawo gobara a cikin kasuwa nan gaba.