Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 7 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 7 ga Watan Maris, 2019

1. Kotu ta bada dama ga Atiku don binciken lamarin zabe

Kotun kara ta rukuni ukku ga lamarin zaben kasa ta birnin Abuja sun bada dama ga dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar don bincike akan kayakin zabe da aka yi amfani da su ga zaben shugaban kasa ta ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, 2019.

Kotun ta gabatar da hakan ne da bukatar dan takaran na cewa a bada  dama ga ‘yan takara don binciken hidimar zaben.

2. Dan takaran Gwamna a Jihar Legas, Agbaje ya karyace zance janyewa daga takara

Jimi Agbaje, dan takaran kujerar gwamna a Jihar Legas daga jam’iyyar PDP ya karyace jita-jitan cewa ya janye daga tseren takaran.

“Karya ne ban janye wa kowa ba daga takaran kujerar gwamnan Jihar Legas” inji Agbaje a wata sanarwa da aka gabatar a ranar Laraba da ta gabata, daga bakin Felix Oboagwina, mai yada labarai ga dan takara.

3. Zan kara kuzari ga shugabanci na ta karo biyu – Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari bayan da aka gabatar da shi a matsayin mai nasara ga lashe tseren shugabancin kasa ta 2019, ya bayyana da cewa zai kara kuzari ga gudanar da aikin sa a matsayin shugaba, a wannan karo ta biyu. Musanman ga samar da tsaro, karfafa tattalin arzikin kasa, samar da ayuka da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Wannan itace alkawarin shugaba Buhari a lokacin da manyan shugabannan Arewa suka ziyarce shi don taya shi murna ga nasarar zaben 2019.

4. Kotu ta dakatar da dan takaran gwamna daga APC a Jihar Taraba

Kotun Koli ta Jalingo, babban birnin Jihar Taraba ta tsige dan takaran gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Sani Abubakar Danladi daga tseren takara ga zaben gwamnoni da za a yi a ranar Asabar ta gaba.

Naija News Hausa ta gane da cewa kotun tayi hakan ne akan zargin cewa dan takaran bai gabatar da ainihin shekarun sa ba.

5. Ralin neman zaben APC a Jihar Akwa Ibom ya karshe da farmaki

Yawon yakin neman zabe na Jam’iyyar APC a Jihar Akwa Ibom ya karshe da farmaki a yayin da aka fado wa mutane da harbe-harben bindiga wajen ralin.

Wani direban Keke NAPEP ya bayyana ga manema labarai da cewa ya gano wasu mutane ukku a ketaren inda aka gudanar da hidimar ralin.

“Na gano su yadda suka sauko daga wata motar Toyota Hilux a ketaren Nsima Ekere, wajen da aka kadamar da hidimar ralin” inji shi

6. Atiku ya mayar da martani aka asusun kudi da aka bude masa

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya mayar da martani akan wata asusu mai likin ‘GoFundMe mutane suka bude masa don taimaka wajen karar zaben shugaban kasa da dan takaran ke yi.

Kakakin yada yawun dan takaran, Mista Paul Ibe, ya bayyana da cewa Atiku bai da sanin asusun amma da cewa ba zai zama da matsala ba idan har mutane su kuddura da taimaka masa da haka akan yakin dimokradiyya.

7. Buratai ya bayyana shirin ‘yan siyasa don tayar da bama bamai ranar zabe

Shugaban Rundunar Sojojin Najeriya (COAS), Lutanar Janar Tukur Buratai, ya gabatar da cewa ya gane da wata shiri da ‘yan siyasa ke da ita na kokarin tayar da bam wajen zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris 2019.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya kamar yadda hukumar INEC suka gabatar da cewa za ta gudanar da hidimar zaben gwamnonin da ta gidan majalisar jihohi a ranar 9 ga Watan Maris, 2019.

8. Kotu da dakatar da dan takara a Jam’iyyar APC daga Jihar Cross River

Kotun koli ta birnin Calabar,  a ranar Talata da ta gabata a Jihar Cross Rivers ta tsige dan takara daga jam’iyyar APC a Jihar.

Kotun, a jagorancin Alkali Eyo, sun dakatar da dan takaran kujerar gwamnan Jihar, Ukpan Odey daga jam’iyyar APC, akan wata laifi da ake zargin sa da ita.

Ka karanta cikakkun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa