Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin MNJTF sun yi nasara da ‘yan ta’addan Boko Haram 33 a yankin Chadi

Published

on

Kakakin yada labarai ga Rundunar Sojojin MNJTF (Multinational Joint Task Force) ta yakin N’Djamena, a Chadi, Colonel Timothy Antigha, ya bayar ga Naija News da cewa Sojojin sun yi nasara ga kashe ‘yan ta’addan Boko Haram 33 da kuma ribato makaman yaki da wasu kayaki dabam dabam.

Inji fadin Mista Timothy, yace “A wata ganawar wuta ta haddin gwuiwar rundunar tsaron kasa ta sama da kasa da ke kasar Kamaru, Nijar da Najeriya suka yi da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Tunbum Rego, da ke kewayan Chadi, rundunar sun samu nasarar kashe ‘yan ta’addan har mutun 33 da kuma ribato bindigogi iri iri da makamai” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rundunar Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 55, sun kuma kubutar da rayuka 760 a Jihar Zamfara

Mista Timothy ya gabatar da cewa sun ribato kayaki da makaman yaki kamar su; Motar yaki biyu, Motar samar da bama-bamai daya, sun lallace motoci tafiya biyu, Bindigar AK 47 guda goma sha biyu, Manyan Bama-bamai, bindiga mai juyi 3736 da dai sauran su.

Ya bayyana da cewa rundunar na shawartan duk masu shirin kadamar da hari ko tayar da farmaki da janyewa da hakan ko kuma su kai ga karshen su idan sun gana da su.

Karanta wannan kuma: Ku Zo mu hada hannu mu gyara Jihar Kaduna – inji Gwamna Nasir El-Rufai