Connect with us

Uncategorized

Ku Zo mu hada hannu mu gyara Kaduna – El-Rufai

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Bayan da hukumar gudanar da zaben kasa ta gabatar da Nasir El-Rufa’i a matsayin mai nasara ga tseren takaran gwamnan jihar sakamakon yawar kuri’u da ya samu kamar yadda hukumar ta bayar fiye da sauran ‘yan takara a Jihar.

Hukumar INEC ta gabatar ne da sakamakon zaben ne da aka yi ranar Asabar 9 ga watan Maris, a ranar Litinin da ta gabata.

A murnan hakan ne Gwamna El-Rufai ya gabatar da bayanin sa game da yadda shugabancin zai kasance a karo ta biyu a Jihar.

Ga bayanin a kasa;

“A cikin wannan lokaci na nasarar zabe, muna mai cewa bai zama da matsala ba a garemu da wadanda basu zabe mu ba, wannan dama ce ga kowa na nuna dan takaran da ya ke so”

“Zamu bada kulawa a garesu, amma dai muna kira garesu da hada hannu damu don gina Jihar Kaduna da ganin cewa Jihar ta samu kai ga cigaba” in ji shi.

“Tun da zabe ya kai ga karshe, lokaci yayi da zamu hada kai da ci gaba da aiki don sake tsarafa jihar mu, Kaduna. Wuraren da akwai matsala sai mu gyara, mu kuma tabbatar da zaman lafiya a Jihar Kaduna”

El-Rufai ya kara da cewa shugabancin sa zai tabbatar da yaki da talauci, karfafa samar da kiwon lafiyar al’umman Jihar, Samar da Ilimin Fasaha, Samar da ayuka ga matasa da kuma samar da isashen tsaro a hukumomin Jihar duka.

Gwamnan ya kuma gabatar da godiyar sa ga jama’ar jihar da irin goyon baya da suka bayar wajen fitowa don jefa kuri’ar su a ranar zabe har da ta kai shi ga nasara, da kuma tabbatar da sabon tarihi da sanya macce a matsayin mataimakin gwamna a Jihar.

“Ko da shike mun fuskanci matsaloli da zargi da dama, duk da hakan bamu raunana ba har sai da muka kai ga nasara don goyon bayan ku. Wannan abin alfahari ne, mun kuma gode maku da bada gaskiya garemu” inji Gwamna Nasir El-Rufai.

 

Karanta wannan kuma: ‘Yan Hari da bindiga sun kashe mutane 16 a Jihar Kaduna a wata sabuwar hari