Connect with us

Uncategorized

Kimanin Mutane 40 suka mutu a harin ‘yan ta’adda a Masallacin New Zealand

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Yau Jumma’a, 15 ga watan Maris, wasu ‘yan hari da bindiga sun kai farmaki a wata Masallacin Jumma’a ta kasar waje, birnin New Zealand inda aka kashe kimanin mutane 40, da yi wa kimanin mutane 20 raunukan bindiga sakamakon watsin harsasun bindiga.

Naija News Hausa kamar yadda muka samu rahoto da cewa an kadamar da harin ne a yayin da ake sallar Jumma’a a kasar New Zealand a yau.

Firayam Minista na New Zealand, Malama Jacinda Ardern, ta bayyana da cewa harin na ‘yan ta’addan ne da kuma fadin cewa “Wannan bakar rana ce ka kasar New Zealand. Ba mu taba fuskantar irin wannan harin ba a kasar nan, kuma muna bakin ciki da hakan kwarai da gaske” inji ta.

Rahoto ta bayar da cewa an kame mutane hudu, Maza ukku da Macce guda da ake zargin su da aikata harin a yayin da aka gano wasu makamai a cikin motar su a kasar lokacin da aka bincike.

Ko da shike an bayar a baya da cewa an saki mutum guda daga cikin su.

Kwamishanan Jami’an tsaron ‘yan sandan kasar, Mike Bush ya umarci kowa da guje wa zuwa Masallaci a kasar har sai abin ya lafa.

“Ku kulle kofunar ku har sai kun karbi umarni daga garemu” inji fadin kwamishanan ga masujadar ChristChurch ta New Zealand.

Karanta wannan kuma: Rundunar Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 55, sun kuma kubutar da rayuka 760 a Jihar Zamfara