Connect with us

Uncategorized

Tsawa ya kashe mutane 3 a Jihar Delta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata mugun tsawa ta kashe mutane 3 a karamar hukumar Ughelli ta Jihar Delta

Naija News ta samu tabbacin hakan ne kamar yadda Kwamishanan ‘yan sandan Jihar ya bayyana ga manema labarai a wata ganawa  a yau Alhamis 21 ga watan Maris.

Kwamishanan, CP Adeyinka Adeleke, ya bayar da cewa ko da shike dagaske ne mutane ukku suka mutu, amma suna kan bincike don abin na da alamar wata mafari, saboda binciken asibiti bai nuna da cewa tsawa ne ya kashe mutanen ba kamar yadda ake zato.

Ya kara da cewa lallai mutane ukku ne abin ya faru da su, ya kuma bayar da sunayan su. Na farkon ana kiran shi da suna Matthew Utuama, na biyun kuma Gabriel Djoma hade da wanit bakanike da ya zo daga garin Onitsha don gyarar wata motar kwasan yashi.

Wani mazaunin wajen ya gabatar ga manema labarai da cewa su ukkun na jiran ne ruwar sama da ake yi ya lafa kamin su fita daga cikin dakin, kamin dada abin ya faru har dukan su suka fadi a mace.

“Su ukkun na jiran ne ruwan sama da ake ya dan lafa kamin su ci gaba da hidimar su, kamin dada tsawar ya dauke su, anan take dukansu kuwa suka mutu” inji shi.

Ya kara da cewa an riga an tafi da gawar Utuama da Djoma a wajen aje gawaki anan Asibitin Tarayya na Otu-Jeremi, “an kuma tafi da gawar bakaniken a garin Onitsha don mikar da shi ga Iyalan sa ko ‘yan uwan sa” inji shi.

 

Karanta wannan kuma: Etsu Patigi, Alhaji Ibrahim Chatta Umar ya mutu bayan rashin lafiyar ‘yan kwanaki kadan.