Connect with us

Uncategorized

Kalli yada kamun wuta ya bar Iyalai 20 da rashin wajen kwanci da kayan zaman rayuwa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A jiya ranar Lahadi, 17 ga watan Maris 2019, wuta ya ci wata anguwa a Jihar Delta inda ya kone a kila gidaje kusan 20 da barin mutanen wajen da kayar da ke a jikin su kawai.

A ganewar Naija News Hausa, bincike ya bayar da cewa gidajen sun kame ne da wuta sanadiyar fashewar risho na gas (Gas Cooker) wanda ake girki da ita a daya daga cikin gidajen da suka kone.

Abin ya faru ne a wata unguwar da ake ce da ita Ugboroke, a nan karamar hukumar Uvwie ta Jihar Delta.

Rahoto ya bayar da cewa abin ya faru ne a missalin karfe 3 na ranar Lahadi a yayin da mutanen gidan suka fita zuwa masujada, wasu kuma sun tafi harkan su.

Ko da shike an bayyana da cewa babu wanda ya ji rauni ko ya mutu sanadiyar kamun wutar, amma dai sun rasa kayakin su duka.

Hukumar Kashe kamuwar wutan yankin su cinma kashe yaduwar wutar kuma amma bisa abin yayi barna da dama.

Wani Mazaunin shiyar ya bayyana ga manema labarai da cewa “Wutar ta kame ne sanadiyar fashewar risho na gas da ake dafuwar abinci da shi wanda wata yarinyar wani mazaunin gidan ke amfani da shi”

“Ba da sanin yarinyar ba, ashe rishon na yoyon gas. kawai ji ta yi abin ya fashe da wuta bayan juyawar ta daga wajen” inji mai bada labarai.

“A guje yarinyar da saurayin ta suka yi wuf daga cikin dakin su a waje don ceton rayuwar su” inji shi.

Abin kaito, mutanen gidan duka sun fita, wasu sun tafi Ikklisiyar su don sujadar ranar Lahadi, wasu kuma sun tafi harkan su.

Daya daga cikin matan gidan da ake kiran ta da suna, Enohor Obukevwo, ta ce “Ban san yadda wutar ya fara ba, amma na rasa komai da nike da shi. Daga ni sai kayan da ke sanye a jiki na kawai” inji ta.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Iyalin mutane shidda sun kone kurmus da wuta a Jihar Kano

Matar ta ce, “Ina kira ga gwamnatin Jihar nan da taimaka mana, da wajen kwana da kuma tallafa mana da abin rayuwa”

Barrack Odjere, daya daga cikin masu zaman shiyar, yace “Na dawo ne kawai daga Masujada sai na tarar da wannan lamarin”

“Dukan kayaki na sun kone kurmus da wuta, na rasa komai, ba inda ni da iyali na zamu hake. Ina kuka ga Gwamnatin da su taimaka mana. muna cikin mawuyacin hali” inji shi.

Kalli hotunan yadda mutane suka koma a kasa;