Connect with us

Uncategorized

JAMB ta daga ranar Fitar da takardan Jarabawa ta shekarar 2019/2020

Published

on

Haddadiyar Hukumar Tafiyar da Jarabawan shiga Makarantan Jami’a Babba (JAMB), ta sake ranar da za a fitar da takardan shiga jarabawan JAMB ta shekarar 2019/2020.

Mun ruwaito da baya a Naija News Hausa da  cewa Hukumar JAMB ta gabatar da ranar jarabawan shekarar 2019.

Mun tuna da cewa ya kamata ne a fara fitar da takardan daga kwamfuta a yau Talata, 2 ga watan Afrilu 2019, kamar yadda Hukumar ta gabatar a baya.

Mai yada labarai ga Hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya gabatar a yau ga menama labarai a birnin Abuja da cewa Hukumar ta daga ranar fitar da takardan gane ranar jarabawa da wajen yin jarabawan zuwa ranar 4 ga watan Afrilu 2019. Watau ranar Alhamis ta makon nan.

Mista Benjamin ya bayyana da cewa hakan ya zamanta ne a yayin da aka daga jarabawan MOCK bisa wasu matsaloli da aka samu, da kuma harin da aka yi wa Ma’aikatan Hukumar.

“Wannan matsalar zai sa dole a canza wajen jarabawan wasu domin magance irin wannan matsalar” inji Benjamin.

Ya kara da cewa Hukumar ta gabatar ne da jarabawan MOCK ne don taimakawa masu rubuta jarabawan JAMB da gane yadda zasu tafiyar da jarabawan su da kuma samun cikakken ganewa bisa hidimar.

“Daya daga cikin dalilan jarabawan MOCK ita ce don magance matsalar makirci da cin hanci da ake samu a wasu santa” inji shi.

“Muna kuma shiri da tabbatar da cewa mun magance duk wata matsalar da zai iya taso a ranar jarabawan”

“Muna rokon dukan dalibai da yin hankuri da mu ga wannan matsalar. Kokarin hukumar itace ganin cewa mun tabbatar da tafiyar da jarabawan a hanyar da ta dace.”