Connect with us

Uncategorized

Matasa sun Kone ‘Yan Hari Biyu da Wuta a Jihar Benue

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu barayi biyu sun fada ga hannun matasa a Jihar Benue

An gabatar da cewa wasu matasa da ke a karamar hukumar Akerior Ushongo ta Jihar Benue sun kone wasu ‘yan hari biyu a fusace bayan da aka gane shirin su.

Abin ya faru ne a shiyar missalin karfe 9:33 na daren ranar Laraba da ta gabata a yayin da barayin suka fada wa shagon wani Iyamiri da ake ce da shi CK a yankin. An bayyana da cewa barayin sun sauko ne a kan babur da harbe-harben bindiga ko ta ina a ga iska kamin dada su fara satan kaya a shagon CK.

Wani mazaunin wajen ya bayyana ga manema labarai da cewa wannan ba itace karo ta farko ba da barayin ke shiga yankin. Da cewa sun saba zuwa bayan sun yi barazanar harbi sai su saci abin da suka ga dama su kuma wuce.

Ya kara da cewa barayin Ukku ne suka fada wa yankin da sace-sacen kayan mutane kamin nan suka hari shagon CK.

“Da Matasan wajen suka gane da haka, sai suka hada kangi suka zagaye barayin har suka samu kame biyu daga cikin su, aka kuma haska masu wuta.” inji shi.
Ko da shike guda ya samu tsira daga cikin su, amma an gabatar da cewa matasan sun samu karbe makamai daga hannun su.

Naija News Hausa ta gane da cewa Shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan yankin Ushongo ya ziyarci wajen da abin ya faru, ya kuma karbi makamai da aka ribato daga hannun barayin ya tafi da shi a Ofishin su don karin bincike.

Ko da shike, Ofisan Yada labarai ga Jami’an tsaron, DSP Catherine Anene, ta bayyana da cewa bai dace ba yadda matasan suka kone barayin, da cewa ya kamata ne bayan da suka kame su, su kuma mikar da su ga jami’an tsaro don hukunci bisa dokar kasa, maimakon kashe su.

“Dokar kasa bata bada dama ga kowa don kisan wani ba ko ta yaya, sai dai yin hukunci bisa doka daga jami’an tsaro” inji fadin DSP Anene.