Uncategorized
#BokoHaram: Mutane 5 sun mutu, Kimanin 45 kuma da mugan raunuka a wata Kunar bakin wake
Kimanin mutane biyar suka rasa rayukan su a wata sabuwar harin ‘yan kunan bakin wake da aka yi a Maiduguri ta Jihar Borno a karshen makon da ta gabata.
Harin ta bar mutane kusan arba’in da biyar (45) da raunuka a yayin da ‘yan ta’addan suka hari wata shiyya da ake ce da ita Muna-Dalti, a garin Maiduguri, babban birni Jihar Borno, a daren ranar Asabar da ta wuce.
A ganewar Naija News, bincike ya bayyana da cewa ‘yan mata biyu ne suka aiwatar da kunar bakin waken.
An bayyana da cewa ‘yan kunar bakin waken sun hari shiyar Muna-Dalti ne da mugayan bama-baman (IEDs) sanye a jikunan su a daren ranar Asabar.
Shugaban Hukumar (SEMA), Kachalla Usman ya gabatar ga manema labarai da cewa lallai harin da gaske ne, kuma mutane biyu sun mutu a yayin da ake nuna masu kulawa a Asibiti.
“A halin yanzu, ana kan bayar da kulawa ta gaske ga wadanda suka samu raunuka a sakamakon harin a babban Asibitin da ke a Maiduguri” inji Usman.
Karanta wannan kuma: Wani Mahaukaci ya Kashe Dan Sanda a Jihar Kwara