Connect with us

Labaran Najeriya

Ba zaka iya zama Shugaban Kasa ba ta bin Kofar baya – APC ta gayawa Atiku

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Alhamis, 11 ga watan Afrilu 2019, Gwamnatin Tarayya na kalubalantar dan takaran kujerar shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Atiku Abubakar, da cewa yayi hankali da matakan da zai jefa shi cikin matsalolin da ba zai iya gane kanshi ba.

Ministan Yada Labaran Kasar Najeriya, Alhaji Lai Mohammed, a wata ganawa da yayi a yau Alhamis da manema labarai a birnin Abuja, ya gabatar da gargadi ga Atiku Abubakar da janye hannu daga matakan da zasu iya sanya shi cikin mugun matsala da ba zai iya fidda kansa ba.

Mista Lai ya gabatar da hakan ne a birnin Abuja a wata zaman tattaunawa hade da Babban Mataimakin musanman ga shugaba Muhammadu Buhari, Mallam Garba Shehu.

“Bai dace ga Atiku da daukan matakan da zasu kai shi ga karya dokar kasa ba a wannan lokaci, da sunan neman yanci da zama shugaban kasar Najeriya, bisa karar da yayi da hukumar zabe game da sakamakon zaben 2019.” inji Lai.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Kotun Kara ta bayar da dama ga Jam’iyyar PDP ta Jihar Kano don kadamar da binciken ga kayaki da takardun da Hukumar INEC tayi amfani da ita wajen hidimar zaben kujerar Gwamna ta Jihar Kano da aka kamala a baya a ranar 9 ga watan Maris 2019.

Minista Lai Mohammed ya kara da cewa “Najeriya kasa ce da ke da dokoki da sharudai. Duk wata matakin da kuma wani zai dauka da zai karya dokar kasar, dole ne a hukunta shi bisa dokar kasa.”