#TVC: Yafi Kyau a Aurar da ‘ya Macce ko ‘Da Namiji da kankanin Shekaru – Akashat Ny’mat

Aurar da karamar ‘ya macce ko kuma auren matashi mai kankanin shekaru a Arewacin kasar mu ta Najeriya bai zama sabon zance ba. Musanman ma akan aurar da yara tun ma basu cika balaga ba.

Akwai wasu Al’adun Aure a wasu Jihohin kasar Najeriya harwayau, daya daga cikin wadannan al’adun itace ‘Kame’. Watau bada ‘ya macce ga aure tun tana ‘yar karama, kamin ma ta gane ko menene aure ko ma kai ga balaga.

Shahararrar ‘yar Watsa labarai a Gidan Talabijin TVC, Akashat Ny’mat ta bada goyon bayan ga yin aure ga ‘ya macce ko ‘da namiji mai kankanin shekaru.

Akashat Ny'mat, TVC, Naija News Hausa, Hausa News, Latest Hausa News, Teenage Marriage in Nigeria

A bayanin Ny’mat, “Yana da kyau a bar ‘ya macce ko ‘da namiji da ke da kankanin shekaru da yin aure, musanman idan an gane da cewa su biyun na da uzurin Jima’i”

“Ko da shike wannan gargadin ba dole sai akan addinin musulunci ba, amma a ganewa na, aurar da su bisa uzurin jima’i shine abu mafi kyau maimakon barin su da shiga karuwanci ko wata halin da bai dace ba” inji Akashat Ny’mat.

Karanta wannan kuma: Wata Macce ta tsage cikin ta da Reza a Jihar Bauchi akan tsanancin zafin haifuwa.