Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumm’a, 19 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 19 ga Watan Afrilu, 2019

1. Shugaba Buhari Rattaba hannu ga dokar biyar Kankanin Albashin Ma’aikata

A ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga takardan doka da yarjejeniyan biyan kankanin albashin ma’aikatan kasa.

Mun ruwaito a Naija News a baya a ranar 19 ga watan Maris da cewa Majalisar Dattijai sun gabatar da takardan dokan biyan albashin ma’aikata na naira dubu 30,000.

2. Kotun Kara ta hana Onnoghen da yin aiki a kowane Ofishi a kasar, na tsawon shekaru 10

Kotun Kara ta birnin Tarayya ta gabatar da wata sabon hukunci ga tsohon babban alkalin Najeriya, Walter Onnoghen, da aka dakatar daga aiki a baya.

Kotun ta gabatar da hukunci daga bakin Alkali Danladi Umar a ranar Alhamis da ta wuce, da cewa Onnoghen ba zai yi aiki ba a kowace Ofishi a kasar har na tsawon Shekaru Goma da nan.

3. Rundunar Sojojin Zamfara sun kame mataimakin Ciyaman na wata karamar hukuma a Jihar

Rukunin Rundunar Sojojin Operation SHARAN DAJI ta Jihar Zamfara sun gabatar da kame mataimakin Ciyaman na karamar hukumar Anka, Mista Yahuza Ibrahim Wuya da zargin cewa yana taimaka wa ‘yan ta’addan Jihar da basu alamu da sakonnani.

Rundunar Sojojin sun gane da hakan ne a wata zargi da aka bayar ranar 13 ga watan Afrilu ta shekarar 2019 da cewa Yahuza na taimaka wa ‘yan ta’addan da ke yankin Wuya.

4. Hukumar EFCC ta sake gabatar da Karar Alkali Ofili-Ajumogobia akan Cin Hanci da Rashawa

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasar Najeriya, EFCC, sun sake gabatar a ranar Alhamis da ta wuce da batun karar Alkali Rita Ofili-Ajumogbia da ke aiki da a Kotun Koli ta birnin Tarayya.

Naija News Hausa ta gane da cewa an yi karar Ofili ne bisa zargin cin Hanci da Rashawa da aka gane da ita.

5. Shugabancin Kasa ta yi watsi ne zargin amfani da EFCC don tsananta wa ‘yan adawa

Shugabancin kasar Najeriya ta bayyana rashin amincewa da zargin da Kungiyar ‘yan neman hakin al’ummar Najeriya (HURIWA) ke yi game da cewa shugaba Muhammadu Buhari na amfani da Hukumar EFCC don hanna ‘yan Jam’iyyar adawa da motsi.

Kungiyar HURIWA sun bada zargi ranar Laraba da ta gabata da cewa Buhari na amfani da hukumomin tsaro don hana ‘yan adawa motsi a kasar.

6. APC/PDP: ‘Yan zabe zasu zabe ni sau dubu bisa kai, Buhari na gayawa Atiku

Shugaba Muhammadu Buhari na barazana da kuma yin izgili ga dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar.

Naija New Hausa ta gane da hakan ne bisa wata bayani na shugaban da cewa ko da sau nawa ne aka yi zabe tsakanin shi da Atiku, shi zai lashe zaben.

7. Bayanin shugaba Buhari game da Hidimar Easter ga ‘yan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na isar da sakon gaisuwa ta musanman akan hidimar Sallar Easter ga ‘yan Najeriya baki daya.

Sakon musanman daga bakin shugaba Buhari ga Kiristocin kasar akan hidimar Easter, ya taya su murna da kuma fatan Alkhairi ga bikin Easter.

8. Kotu ta tsayar da karar tsige Saraki da Dogara zuwa gaba

Kotun kara ta birnin Tarayya ta daga karar da ake game da Shugaban Sanatocin Najeriya, Bukola Saraki da kakain Gidan Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara zuwa gaba.

and 52 other lawmakers, has today been adjourned by a Federal High Court Abuja till April 30.

Kotun ta dakatar ne da karar har zuwa ranar 30 ga watan Afrilu da ake cikin ta.

9. Shugabancin kasa ta gabatar da ranar da za a fara biyan kankanin albashin na dubu 30,000

Bayan da shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga dokar biyar kankanin albashi ga ma’aikatan kasa, shugabancin kasar ta gabatar da cewa ba zata yi jinkiri ba da fara biyan kudin.

An gabatar da hakan ne a gabatarwan shugabancin kasar a ranar Alhamis da ta gabata, bisa shugaba Buhari ya amince da takardan, da kuma rattaba hannu.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com