Connect with us

Uncategorized

Gobarar wuta ya Kone wajaje biyu a Makarantar Jami’ar Aliero ta Jihar Kebbi

Published

on

at

advertisement

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa Gobarar wuta ya kone wajen kwanan Maza ga ‘yan Makarantan Jami’a ta ‘Kebbi State University of Science and Technology, Aliero’, bisa wutan ya kame gefe guda na ajin karban karatu na Jami’ar.

Bisa ganewa bayan bincike, an bayyana da cewa gobarar wutan ya auku ne sakamakon tabuwar hadewar wayan wutan lantarki a gefe guda ta Jami’ar.

“A hakan dai gobarar ta kone sashin Dakin koyaswa na Ilimi da kuma Dakin Barci ta Maza da ke kusa da wajen, kamin a baya aka samu cin nasara da kashe yaduwar wutan”

Daya daga cikin Manyan Mallaman Makarantan Jami’ar, ya bayyana ga manema labarai da cewa Hukumar Makarantar ta kafa Kwamitin Bincike akan Hidimar don gane ainihin yadda gobarar ta fara da kuma magance duk wata matsala a zai iya biyo baya.

“Abin takaici a ganewa da cewa karo ta biyu kenan da gobarar wuta ke barna a cikin Makarantan Jami’ar, kuma ba a samu magance hakan ba har sai da wutan yayi muggan barna” inji shi.

Gwamnan Jihar, Abubakar Atiku Bagudu, a ziyarar da yayi a makantan Jami’ar ranar Litini da ta wuce, ya bada tabbacin cewa ya dauki nauyin sake gyara da tsarrafa ginin da gobarar wutan ya lallace.

Karanta wannan kuma; Yafi Kyau a Aurar da ‘ya Macce ko ‘Da Namiji da kankanin Shekaru – Akashat Ny’mat