Uncategorized
Makarantan Jami’ar College of Science and Technology ta Jihar Kebbi ta kori ‘yan madigo Hudu
Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda aka kori wasu ‘yan madigo hudu a makarantar Jami’ar Kebbi state College of Science and Technology.
Bisa bayanin Babban Malami da kuma mai jagorancin Makarantan Jami’ar da a Turance ake kira ‘Povost’, Mista Aminu Dakingari ya bayyana da cewa masu tsaron makarantar, tare da masu tsabtace makarantar ne suka gane da ‘yan matan a lokacin da suke kokarin yin madigo da junar su a dakin barcin dalibai.
A yayin da Dakingari ke bayani da manema labarai a karshe makon da ta wuce, ya gabatar da cewa kwamitin hukunta masu laifi a jami’ar, sun gane da kuma tabbatar da lallai ‘yan matan sun aikata laifin madigon, watau (kwanciyar ‘ya mace da mace) da ake zargin su da ita, sun kuma amince da hakan bayan da ake tuhume su.
“Daliban su amince da zargin da ake da su kuma mun riga mun koresu daga Jami’ar. A baya daliban sun aiko mani da wata sakon barazanar kashe ni da kuma cin mutunci na, amma dai hukumar tsaro da riga ta dauki matakin musanman da hakan” inji fadin Dakingari a Ofishin sa.
Ya kara bada haske da cewa biyu daga cikin ‘yan matan, ‘yan garin Kontagora ne a Jihar Neja, sauran kuma daga Jihar Sokoto da Kebbi.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Wata ‘Yar Shekara 19 ta kashe Yayanta a Jihar Kano bayan da gardama ya tashi tsakanin su a wajen hidimar liyafan auren ‘yar uwansu.