Connect with us

Uncategorized

Mutuwa rigan Kowa! Maman Sanata Dino Melaye ta riga mu zuwa Gidan Gaskiya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanatan da ke Wakilcin Jihar Kogi a  Gidan Majalisar Dattijai, Dino Melaye, ya rasa tsohuwar sa, Deaconess Comfort Melaye.

Naija News Hausa ta gane da cewa Maman Sanatan ta mutu ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu da ta gabata. Ko da shike dai ba tabbacin sanadiyar mutuwar ta, ko kila hadari ne ko kuma rashin lafiyar jiki, amma dai abin da muka sani itace, rana ya cika a gareta.

Dino Melaye bai jinkirta ba da sanar da hakan a shafin yanar gizon nishadarwa ta Twitter a daren ranar Alhamis da ta wuce.

Ga bayanin Sanatan a kamar haka, “Girma da Daukaka ga Allah Sarkin Runduna, Ina mai gabatar maku a wakilcin Iyalin Melaye da cewa mun rasa Maman mu Deaconess Comfort Melaye. Mun gode da irin rayuwar da ta yi a duniya kamin cikawa, mun kuma gode ga Allah da rahaman sa a garemu duka, Tsohuwana, Abokiyar hira na, na rasa ki kwarai da gaske, Godiya ga Allah.”

Kalli sakon a layin Twitter;