Connect with us

Labaran Najeriya

‘Yan Hari da Bindiga 150 sun hari kauyen Katsina da kashe kimanin mutane 15

Published

on

Naija News Hausa ta karbi rahoto da cewa kimanin mutane 15 sun rasa rayukan su a wata sabuwar hari da ‘yan hari da makami suka kai a Jihar Katsina ranar Alhamis da ta gabata.

An bayyana da cewa ‘yan harin sun kai kimanin mutane 150 akan babura, suka kuma fada wa kauye biyu a Jihar Katsina da kashe mutane 15, da kuma sace Shanayen su bayan kone masu gidaje, bisa bayanin da Jami’a tsaro suka bayar ga Naija News.

Manema Labaran AFP sun bayyana a binciken su da cewa harin ya faru ne a kauyuka biyu, watau kauyan Gobirawa da kauyan Sha Ka Wuce, a Jihar Katsina, tsakanin asuba’in ranar Laraba da ta wuce.

Kakakin yada yawun hukumar Jami’an tsaron Jihar, Gambo Isah, ya bayyana da cewa an riga an watsar da Jami’an tsaro a shiyar don bincike da neman kama wadanda suka aiwatar da wannan mugun abin.

Ko da shike Shugaba Muhammadu Buhari da ya zama ainihin dan Jihar Katsina, ya bada umarni ga hukumomin tsaro don tabbatar da cewa sun dakatar da matsalar hari da ‘yan ta’adda ke kaiwa a Jihar Katsina.

KARANTA WANNAN KUMA: Boko Haram sun kai sabuwar hari da kashe mutane 14 a yankin Monguno ta Jihar Borno