Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 6 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 6 ga Watan Mayu, 2019

1. Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Amurka

A ranar Lahadi da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga ziyarar kai tsaye da ya kai zuwa kasar UK ‘yan kwanaki da suka gabata, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa.

An bada tabbacin dawowar shugaba Buhari ne daga bakin Mista Femi Adesina, Mataimakin shugaban kasa wajen lamarin sadarwa.

2. Daliban Makaranta sun roki Hukumar JAMB da sakin sakamakon Jarabawan su ta shekarar 2019

Wasu daga cikin Dalibai da suka zauna ga rubuta jarabawan shiga babban Makarantar Jami’a (JAMB), sun yi kira ga Hukumar JAMB da su saki sakamakon jarabawan su da suka rubuta ‘yan kwanaki da suka shige.

Naija News ta gane da hakan ne bisa ganawar da manema labarai suka yi da wasu daga cikin daliban da ke shiyar Bwari, a ranar Lahadi da ta wuce.

3. Hukumar EFCC ta kafa kai ga binciken Bukola Saraki

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC sun tada wata sabuwar bincike na neman zargi ga sanata Bukola Saraki, akan albashi da kudaden da suka shiga asusun shi tun lokacin da ya hau kujerar Gwamnan Jihar Kwara a shekarar 2003 zuwa 2011.

Naija News Hausa ta tuna da cewa Sanata Bukola Saraki ya fadi ga zaben neman komawa kujerar Sanata a Jihar Kwara ga zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar PDP.

4. Wasu ‘Yan Biafra sun ki amince da dokar Zama daki Kulle da shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya bayar

Dokar da shugaban Kungiyar Iyamirai ta Najeriya (IPOB) da ke yaki da neman yancin Biafra ya bayar bai zama da kafuwa ba, a yayin da wasu suka ki bin dokar.

A baya Kungiyar IPOB ta sanar ga mambobin ta da cewa zasu kadamar da dokar zama daki kulle a ranar 30 ga watan Mayu ta shekarar 2019 don tunawa da tarihi da kuma yadda aka kashe mambobin kungiyar shekarun baya da suka wuce.

5. APC/PDP: Dalilin da yasa Buhari ba zai zama da kwanciyar hankali ba – Shehu Sani

Sanatan da ke Wakilcin Jihar Kaduna a Gidan Majalisar Dattijai, Shehu Sani ya kalubalanci Jam’iyyar APC da yadda suka kadamar da makirci a zaben 2019 don mayar da kansu a kan shugabancin kasar Najeriya.

Sanata Shehu yace, “shugaba Buhari ba zai iya buga gaba da cewa irin gurbin da yake so ya bari a kasar Najeriya ke nan ba a matsayin shi na shugaba, da irin makirci da aka kadamar da shi a zaben kasar da aka kamala a baya.

6. Boko Haram sun sake mamaye wata yanki a Jihar Borno

Wasu ‘yan ta’adda da ake zargin su da zama ‘yan ta’addan Boko Haram, sun sake mamaye wata yanki a Jihar Borno.

Naija News ta samu rahoto da cewa ‘yan ta’addan sun hari wata shiya a karamar Magumeri ta Jihar Borno a ranar Lahadi da ta gabata.

7. Kasar Najeriya ta tuna da cikar shekara 9 da Tsohon shugaban kasa, Yar’Adua ya Mutu

Al’ummar Najeriya na tunawa da tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar’Adua, da ya mutu a kan mulki shekarar 2010 da ta gabata.

Wannan itace shekara 9 da tsohon shugaban kasar ya mutu a yayin da yake kan shugabancin kasar.

8. Sultan ya sanar da Ranar da za a fara hidimar Ramadan ta shekarar 2019

Mai Martaba, Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar III, ya gabatar ga Musulunman Najeriya da cewa Azumin watan Ramadan ta shekarar 2019 zai fara a ranar Litini, 6 ga watan Mayu.

Wannan ya biyo ne bayan an sanar da gane fitar watan Ramadan a Sokoto, a maraicen ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu da ta gabata.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com