Connect with us

Uncategorized

Bayanin Mai Martaba, Sultan na Sokoto game da watan Ramadan ta shekarar 2019

Published

on

at

advertisement

A wata gabatarwa ta maraicen ranar Lahadi, 5 ga watan Mayu da ta gabata Jihar Sokoto, Mai Martaba, Sultan na Sokoto, Sa’ad Abubakar III ya gargadi dukan ‘yan uwa Musulunman Najeriya da cika da addu’a ga kasar Najeriya, a nemi albarkan Allah akan dukan hidimar shugabancin kasar da kuma zaman Lafiya da Zumuncin Al’ummar kasar.

Naija News Hausa ta gane da cewa wannan bayanin Sarki Abubakar ya biyo ne bayan da aka sanar da gani sabon watan Ramadan a Jihar Sokoto, da maraicen ranar Lahadi da ta wuce.

An gabatar da sanarwan ne daga hannun Kwamitin ganin wata na Najeriya, a wata sanarwa da aka wallafa jawabin Sarki Sultan a shafin Twitter; inda sarkin ya umarci jama’a da su tashi da azumi ranar Litinin.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Saudi Arabia ta sanar da cewa duk wani da ya gane da fitar Watan Ramadan a ko ta ina ya je ya sanar a Kotun da ke kusa da shi don bada tabbacin hakan.