Uncategorized
Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya Kara ga Sarautan Jos
Gwamnatin Jihar Filato ta rabar da Kujerar Sarautan Jos, ta cire Arewacin Jos da kuma Sarautan Riyom daga hadaddiyar sarautan Jos da ke a karkashin jagorancin Gbong Gwom na Jos, Yakubu Gyang Buba.
Ka tuna cewa Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Kotun Koli ta Tsige Sarakai Hudu da Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano ya kafa.
A can baya, Gwamna Simon Bako Lalong, a watan Agustan da ya gabata, ya kirkiro wasu sabon shugabanni da kuma inganta wasu, hade da Sarautan Anaguta ta Arewacin Jos da kuma Aten na Ganawuri a Riyom.
Gwamna Simon Lalong ya kara gaba da bayar da babban Sarautan Jagora na farko ga Ujah na Anaguta da kuma Atar Aten na Ganawuri.
Naija News Hausa ta tuna da cewa ko da shike Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano ya bayyana cewa ya dauki matakin kara kujerar sarauta hudu ne a Jihar Kano don karfa tattalin arzikin jihar da kuma samu sauki wajen yaki da ta’addanci a Jihar.
Duk da hakan, Al’ummar Najeriya sun zargi Ganduje da yin hakan ne don cin mutuncin Sarki Muhammad Sanusi II, da ke wakilci da zaman sarkin tarayyar Jihar Kano.