Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 20 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 20 ga Watan Mayu, 2019

1. APC Ba ta zaman komai ba tare da ni ba – inji Okorocha

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha na barazanar cewa Jam’iyyar APC a Jihar Imo ba ta zaman komai ba tare da shi ba.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Okorocha ya bayyana hakan ne don mayar da wata martani ga bayanin Daraktan na Muryan Najeirya (VON) da kuma Jigo a Jam’iyyar APC, Mista Osita Okechukwu yayi na cewa Gwamnan ya lallace tasirin Jam’iyyar APC a Jihar Imo.

2. Atiku yayi Barazanar Karar Ma’aikacin shugaba Buhari da bukatar shi da biyan N500m

Dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya daga Jam’iyyar PDP, a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya gabatar da bukatar Lauretta Onochie, Ma’aikaciya ga shugaba Muhammadu, da rokon sa da kuma biyan kudin bacin suna na naira Miliyan N500m.

Atiku ya gabatar da hakan ne a wata wasika da aka wallafa a ranar 14 ga watan Mayu, da kara barazanar cewa idan Lauretta ta kaurace wa bukatan sa, zai gabatar da karar ta da biyan naira Biliyan N2m.

3. Karya ne Buhari baya a Mecca – inji Nnamdi Kanu

Shugaban Kungiyar ‘yan yaki da neman yancin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, na zargin cewa lallai shugaba Muhammadu Buhari baya a Makkah, ta Saudi Arabia.

Ka tuna da cewa mun sanar a Naija News a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya karbi wata gayyata daga sarkin Saudi Arabia, Salman Bin Abdulaziz.

4. Joshua Dariye ya karbi naira Miliyan N171m a kurkuku

Tsohon Gwamnan Jihar Filatu, Sanata Joshua Dariye, ya ci gaba da karban kudin wata na naira dubu N750, 000 da kuma kudin kashe-kashe na kimanin naira Miliyan N13.5m, a kowace wata daga gidan Majalisar Dattijai.

Sanatan na karban hakan ne duk da cewa yana a dakile a tsawon watannai 11 a kurkuku.

5. PDP: Atiku ya gabatar da sabuwar bukata a Kotun Kara

Jam’iyyar PDP da dan takaran su ga zaben shugaban kasar Najeriya a shekara ta 2019, Atiku Abubakar, sun gabatar da sabuwar bukata ga Kotun Kara, don samun daman bincike ga Na’ura da Kwamfuta da Hukumar INEC ta yi amfani da ita a wajen hidimar zaben watan Fabrairu da aka yi a baya.

Wannan karin kara ne bisa zancen Atiku da Jam’iyyar PDP na kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari a  zaben watan Fabrairun ta 2019.

6. Ka fito da shaidar zance da zargin da kake yi, Atiku ya gayawa Lai Mohammed

Atiku Abubakar ya kalubalanci Ministan Yadar da sanarwai, Lai Mohammed da bayar da shaidan akan zancen da yake na cewar Atiku da Jam’iyyar PDP na kadamar da shirin tsige shugaba Muhammadu Buhari.

Ka tuna da cewa Atiku ya gabatar da karar rashin amincewa ga Kotu akan sakamakon zaben 2019.

7. Kotu ta gabatar da ranar kafa baki ga zancen Mutuwar Sanata Isiaka Adeleke

Kotun Koli ta Jihar Osun da ke a garin Ede ta gabatar da ranar 6 ga watan Yuli don kafa bincike ga sanadiyar mutuwar gaugawan Isiaka Adetunji Adeleke, Sanata da ke wakilcin yankin Jihar Osun.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa sanarwan Alkali da ke jagoran Karar, Ayo Oyebiyi.

8. Saraki zura ido ga kujerar zaman Minista a Jihar Kwara

Gbemisola Saraki, diyar marigayi, tsohon jigo a Jam’iyyar APC a Jihar Kwara, Olusola Saraki, da kuma tsohon sakatare ga Jam’iyyar, Alhaji Lai Mohammed sun zura ido ga neman kujerar Minista a Jihar Kwara.

A zaman ‘yan kasa da Jiha, su biyun, Gbemi Saraki da Lai Mohammed sun zura wa kujerar Minista ido a Jihar Kwara a karkashin shugabancin Shugaba Muhammadu Buhari a karo ta biyu.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com