Connect with us

Uncategorized

Kotun Majistire ta Jihar Kano ta bada Umarni kame Mutane Ukku hade da Sanusi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A yau Talata, 28 ga watan Mayu 2019, Kotun Majistire ta Jihar Kano ta bayar da umarnin a kame wasu mutane uku hade da Mannir Sanusi, babban ma’aikaci ga Sarkin Jihar Kano, Muhammadu Sanusi II.

A fahimtar Naija News Hausa, an bayyana cewa Kotun ta bukaci kame su ne akan wata zargin Cin Hanci da Rashawa da kuma Makirci na Naira Biliyan Hudu (N4b) da aka gane da su, aka kuma bukace su da bayyana a gaban kotu don neman bayani amma suka kaurace wa hakan.

Babban Alkalin Kotun, Mohammed Idris ne ya bada umarnin cewa a kame Sanusi mai wakilci da sarautan Damburan Kano, Mujitaba Abba, da kuma Magatakardan Asusun Kwamitin Sarautar Kano, Sani Muhammad-Kwaru, akan kauracewar su ga kirar da Kotu ta yi a garesu.

Mista Idris ya rattaba hannu da kuma bada umarnin ne bisa gargadin da Salisu Tahir, mai bada shawarwari ga kwamitin ya bayar.

A bayanin Ciyaman na Kwamitin Sarautar Jihar, Mista Muhiyi Magaji ya bayyana cewa su ukun ne ake da tabbacin kadamar da makirci akan zancen naira biliyan hudu din da aka rasa.