Connect with us

Labaran Najeriya

2019: Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da Asusun Sa ga Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Hidimar Rantsar da Muhammadu Buhari

A ranar Talata da ta wuce, shugaba Muhammadu Buhari ya mikar da takardan da ke dauke da asusun arzikin sa kamin sa’o’i kadan da hidimar rantsar da shi a shugabancin kasar a karo ta biyu.

Bisa bayanin da Garba Shehu, mataimakin shugaba Buhari wajen al’amarin sadarwa ta hanyar yanar gizo ya bayar, ya bayyana cewa shugabn ya mikar da asusun kudin sa ta da ga Hukumar Code of Conduct Bureau (CCB), kamar yadda dokar kasa ta bayar kami a rantsar da shi a karo ta biyu ga shugabancin kasa.

Naija News Hausa ta  fahimta da cewa Mista Sarki Abba, Mataimakin shugaba Buhari a al’amarin Aikace-aikacen gida ne wakilci Buhari wajen mikar da takardan gabatar da asusun ga Ciyaman na Hukumar CCB, Farfesa Mohammed Isa.

Bisa rahotannai, asusun da shugaban ya gabatar a wannan shekara bai banbanta ba da wadda shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar a shekara ta 2015 da ya shiga mulkin farar fula a karo ta farko.

“Babu sabon gida, sabon Asusun Banki a kasar waje ko a Najeriya, babu wata sabon kadamar ta kansa”

Ciyaman na Hukumar CCB, Mista Mohammed Isah ya jinjina da rattaba wa shugaba Muhammadu Buhari da nuna kansa a matsayin shugaba da jagora na kwaran gaske, musanman gabatar da asusun sa kamar yadda dokar kasa ta bayar ba tare da jinkirta ko wata matsala ba.

KARANTA WANNAN KUMA: Kotun Majistire ta Jihar Kano ta bada Umarni kame Mutane Ukku hade da Ma’aikacin Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II.